'Yan adawa sun samu rinjayen kafa gwamnatin Isra'ila
June 3, 2021Kawancen jam,iyun adawa a Isra'ila sun amince da kafa gwamnatin gamin ganbiza da za ta kawo karshen mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu da ya yi shekaru 12 yana jan zarensa, masharhanta na cewa ba girin girnba dai, ta yi mai. Tsohon ministan tsaron Isra'ila mai ra'ayin rikau, wanda ada na hanun daman Netenyahu ne, Naftali Bennett ne dai zai zama sabon firaministan na tsawan shekaru biyu, wanda za yi karba-karbar kujerar da shugaban jam'iyar masu sassaucin ra'ayi ta Green White Party Yair Lapid karkashin wannan kawance.
Sanar da wannan kawancen ke da wuya dai, Netenyahu ya dirar mikiya kan tsofin kawayensa masu matsanancin ra'ayi da suka yaye masa baya suka kulla kawancen da masu sassaucin ra'ayi.
Karin Bayani:Benjamin Netanyahu ya gaza kai bantensa
Wasu daga cikin Masharhanta dai na ganin cewa, har yanzu ruwa bai karewa dan kada ga Netenyahun, kadan akai la,akari da irin mummunan sabanin akidar dake tsakanin jam,iyun wannan kwancen. Gamayyar jam,iyun larabawan dake zaune a Isra,ila dai, karkashin jagorancin Abbas Mansur ta shiga cikin wannan kawancen da ake yi wa take da Kawancen sauyi, to sai dai masharhanta irin Dr Ibrahin Hakeem, da ke sharhi kan alakar Yahudawa da Falalsdinawa na ganin cewa Larabawan sun yi shuka a idon makwarwa.
Cikin tsukin mako guda ne dai majalisar dokokin Israela, Knesset da ke da membobi 120 za ta kada kuri,ar amincewa da wannan gwamnatin gami ganbizan ta yan adawa,idan kuwa har aka samu kasa da kuri'u 80 da ke goyan bayan hukumar,to za a sake shirya wani zabe a kasar da zai zama karo na biyar cikin tsukin shekaru 2.