Takaddama tsakanin China da Taiwan
September 18, 2023![](https://static.dw.com/image/66315697_800.webp)
Talla
Wata sanarwar offishin minstan cikin gida na Taiwan ta ce, ci gaba da yin barazanar na sojojin China zai iya haifar da tashin hankali da tabarbarewar tsaro a yankin. Ma'aikatar cikin gidan ta Taiwan ta yi gargadin, tana mai kira ga hukumomin China da su dakatar da wadannan munanan ayyuka da suka kira tsokana. Tun a shekara ta 1949 kasashen biyu ke yin rikiciwandaChina ta yi ikirarin cewar yankin mallakarta ne.