1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan kalamun Shugaba Macron

Abdoulaye Mamane Amadou
August 27, 2022

Turkiyya ta yi fatali da zarge-zargen Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cewa tana da hannu game da boren kin jinin Faransa a wasu yankuna na nahiyar Afirka.

Frankreich Algerien Präsident Macron trifft Präsident Tebboune
Hoto: Eliot Blondet/abaca/picture alliance

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan yammaci ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce "kalaman Shugaba Macron zance ne irin na 'yan matan amarya, duba da irin rawar da Faransar ta taka a yayin mulkin mallakarta a wasu kasashen nahiyar.

A jiya ne dai albarkacin ziarar aikin da ya kai a Aljeriya, Shugaba Macron ya zargi wasu kasashen duniya ciki har da Rasha da China da Turkiyya da hannu wajen ingiza wutar kin jinin Faransa da ta karade nahiyar Afirka ta hanyar amfani da wasu matasa, kalamun da kuma tuni suka bar baya da kura.