Kalubale kan isar da kayan agaji Siriya
March 1, 2018Motocin Majalisar Dinkin Duniya dauke da tulin abinci da magunguna sun kasa samun damar shiga don sauke kayyakin masarufin a sanadiyar barin wutan da ake ci gaba da yi duk da cewa an cimma yarjejeniya na tsagaita bude wuta a yankin gabashin Ghouta da ke ci gaba da kasancewa a karkashin ikon 'yan tawaye masu adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.
Kwanaki hudu kenan da cimma yarjejeniyar bayan wani zama da aka yi da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda Rasha ta amince ta dakatar da kai hari na tsawon wata guda, lamarin da ake ganin ya zama dole kafin a iya kwashe marasa lafiya dama wasu da suka sami rauni. Wani babban jami'i a hukumar bayar da agajin Mark Lowcock ya nemi mambobin majalisar da su yi duk mai yi yiwuwa don ganin a mutunta dokar.