Kalubalen adawa mai karfi a Najeriya
July 30, 2025
Sabon zargin dai na iya jawo cikas bisa makomar ADC da ke dada samun farin jini da kila tsorata 'yan mulki na kasar.
Wata wasikar wani jigon jam‘iyyar Salihu Lukman ce ke neman yamutse hazo cikin jam'iyyar inda ra‘ayi ke dada nuna alamun rabuwa bisa salon shugabancin ADC. Jam'yyar da ke zama babban fata ga adawar amma kuma ke fuskantar wani sabon rikici. Lukman din dai yayi gargadin yunkurin wasu kalilan na kwace ragamar jam'iyyar da nufin cika burin mulki a shekara ta 2027
Duk da cewar har ya zuwa yanzu tana mataki na riko cikin batun shugabanci a matakai daban daban, ko bayan Lukman din ana ta kara nuna damuwa bisa salon mulkin ADC a matakai daban daban
Dr Umar Ardo jigo ne a cikin jam'iyyar ADC da yace tun daga farkon fari ADC ta kafu ne bisa tsarin da ke nuna alamun karkata zuwa ga kalilan.
Kokarin sanin halin kowa a cikin rani, ko kuma neman ceton demokaradiyyar Najeriya, gwagwarmaya ta mallakar jam'iyyun ne dai dama ta kai ga mafi yawa na yayan ADC sauyin sheka daga jam'iyyun su na asali. Gwagwarmayar kuma da ke kara fitowa fili yanzu.
Shi kansa shugaban jam‘iyyar na kasa Sanata David Mark ya dauki lokaci yana lallashi a kokarin hada kai a tsakanin magoya baya.
Solomong Dalung dai jigon jam'iyyar ne a Plateau da kuma yake fadin ADC bata shirin fadawa aljihun wani.
Tun daga farkon fari dai dama an rika mamakin haduwar da ke kama da taro na wuta da shiba a cikin inuwar jam'iyyar ADC.
A baya dai an dauki shekaru ana kallon kallo na siyasar kafin barazanar Bola Ahmed Tinubu cikin fagen siyasar ta tilasta hadakar da ke kama da zaman kishiyoyin dauri
Ibrahim Mohammed Gamawa mai sharhi cikin batun siyasar kasar, ya ce an dade ana ta hasashen rikicin da ke zaman zakaran gwajin dafi na dorewar ADC.
'Yan kwanaki da kila watanin da ke tafe na iya tasiri ga kokarin karin karfin jam'iyyar da kila ma nasarar ta kokarin neman mulkin kasar.