Nijar: Matsala a aikin hakar uranium
September 11, 2023Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin fafutuka a Jamhuriyar ta Nijar, suka fara kira ga sababbin hukumomin mulkin sojan kasar da su sake duba yarjejeniyar aikin hakar makamashin na uranium da kamfanin Orano na kasar Faransa. Tun dai bayan juyin mulkin sojoji ne, bayanai daga yankin Agadez da kamfanin Orano mallakar Faransa ke aikin hakar Uranium, ke cewa aikin na fuskantar tafiyar hawainiya sakamakon wasu matsaloli masu nasaba da takunkumin karya tattalin arzikin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da UEMOA suka kakabawa kasar. Babban magatakardan kungiyar Kodago ta Ma'aikatan Kamfanonin Hakar Uranium ta Kasa Malam Abbas Moukaila ya tabbatar da wannan batu ga manema labarai, yana mai cewa matsalar ta ma shafi fitar da uranium din zuwa kasashen waje.
Da yake tsokaci kan halin da aikin hakar uranium din ya shiga tun bayan juyin mulkin, jami'in kungiyar ROTAB da ke sa ido kan aikin hakar ma'adinai a Nijar Malam Ilyassou Aboubacar shawara ya bayar ga sababbin hukumomin kasar da su dauki matakin sake yarjejeniyar hakar karfen uranium da kamfanin na Orano na Faransa. Wasu bayanai na baya-bayan nan na nuni da cewa tun a ranar Jumma'a takwas ga wannan wata na Satumba da muke ciki, kamfanin na Orano ya dauki matakin dakatar da aikin hakar uranium din baki daya a sakamakon matsalolin yankewar kayan aikin. Wannan dai ka iya zama wata babbar asara ga sabuwar gwamnatin Nijar din, wacce ke cikin yanayi na tsananin bukatar kudin shiga.