1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tarin bashi da ke kan jihohi

September 18, 2024

Can cikin lissafin ka dai, kudin shiga suna neman ninkawa. To sai dai kuma daga dukkan alamu rikicin na neman ninka wa, cikin jihohin Tarayyar Najeriya da ke samun karin kudin shiga amma kuma suke tangal-tangal.

Najeriya | Naira | Tsadar Rayuwa | Bashi
Gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohin Najeriya, na ci gaba da ciyo bashiHoto: Ubale Musa/DW

Ko a cikin wannan mako dai, matakan mulkin Najeriyar uku sun raba adadin da ya kai triliyan daya da miliyan dubu 200 a tsakaninsu. Abun da ke ta nuna alamun sauyi cikin batun kudi, a daukacin kasar da ta zare tallafin man fetur a cikin fatan samun karin kudi na harkokin al'umma. To sai dai kuma duk da karuwar kudin, jihohin na kuma kallon karin rikici cikin mafi yawan harkokinsu. Sai da ta kai wasu jihohi 20 ciyo sababbin basukan da suka kai kusan Naira miliyan dubu 440, a cikin watanni shida na farko a shekarar bana da nufin iya sauke nauyin tafi da harkokin al'umma.

Karin Bayani: IMF ya bukaci janye tallafin lantarki

Cikin tsakiyar rikicin dai, na zaman wani dimbin bashin da ke zaman kaya cikin wuya na jihohin. Bashin kuma da a cewar Farfesa Muttaqa Muhammad Usman da ke zaman kwararre a fannin tattalin arziki, ke fuskantar matsala sakamakon faduwar darajar kudin kasar Naira. A jihohi kamar Kaduna da Ondo da Osun da ma Cross Rivers dai, daukacin kudin shigar na tafiya ne a wajen biyan ruwa na basukan da ke kansu a yanzu. Ga misali dai ana bin jihar Kaduna dalar Amurka miliyan 587, ko bayan Naira miliyan dubu 85 da ma bashi na masu kwangila na naira miliyan dubu 115.

Darajar kudin Najeriya Naira, na kara faduwaHoto: DW

Ibrahim Jibo dai na zaman tsohon kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki a Zamfara, kuma ya ce cin bashin na zaman wajibi ga jihohi da ke da kayyadaddun hanyoyin samun kudin shiga. Bashi hanji ko kuma kokari na burge da dama dai, ana zargin jihohin kasar da kasa mai da hankali ga bukata wajen kisan kudin al'umma. Ya zuwa yanzun dai ga misali, mafi yawan jihohin arewacin kasar na gasar ginin gadoji tare da mantawa da bangaren ilimin da ke da tasiri ga rayuwa da makomar al'umma.

Karin Bayani: Wa ke morar agajin gwamnati a Najeriya?

Dakta Hamisu Ya'u dai na sharhi kan tattalin arziki da harkar mulkin, kuma ya ce an raba gari a tsakanin gwamnonin jihohin da kokarin inganta harkokin al'umma. Kowane lokaci daga yanzun dai, ana shirin fuskantar wani sabon rikici a tsakanin jihohin da ke gwagwarmaya ta rayuwa da ma'aikatan da ke da fatan samun mafi karancin albashin naira dubu 70 a daukacin kasar. Jihohi da yawa dai, na jan kafar rashin kudin sauke alkawari na masu kodagon da ke zaman kafa daya tilo ta tayar da hankalin 'yan mulkin Najeriyar a halin yanzu.