1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS cikin halin tsaka mai wuya

Uwais Abubakar Idris AH
December 11, 2023

Kungiyar kasashen Afrika ta yamma Ecowas na fuskantar kalubale na hadin kai a tsakanin kasashen kungiyar, inda uku daga cikin kasashen da sojoji ke mulki suka kafa sabon kawance na tsaro.

Hoto: Kola Sulaimon/AFP

 Kungiyar bunkasa tattalin arziki ta kasashen Afrika ta yamma ta samu kanta a wannan mumunan hali na gaba kura baya siyaki, domin baya ga koma bayan tattalin arziki da matsalar rashin tsaro ta ta’adanci da ta adabi kasashe da dama, sai ga wannan rarrabuwar kawunan da ta kuno kai biyo bayan kuts ne da sojoji suke yi a kasashen kungiyar. Tirjewar da Jamhuriyara Nijar ta yi tare da kula sabon kawancen tsaro na yankin Sahel da kasashen Jamhuriyar Nijar, Mali da Burlkina Faso suka yi ya nuna akwai abin da suka taka. Dr Faruq Bibi Faruq masanin kimiyyar siyasa da ke Abuja ya bayyana man yadda yake hangen lamarin. ‘’Wanna barazana ce ga kungiyar Ecowas kuma tarihi ne yake neman maimaita kansa, domin an taba samun irin hadaka a tsakanin kasashen Misra da Syria da Iarki a 1958. Tasirin yana da  matsala a wancan lokaci saboda kasashe ne masu yanci. To sai dai halin da kasashen ke ciki kawanci na iya zama matsala sosai ya yi tasiri a tafiyar da suke yi a yanzu. Wannan  ya nuna cewa siyasar yanki  Afirka ta yamma ta dauko wani sabon launi wanda in ba’a yi hankali ba za ta iya rusa   hada kan da ake da shi’’

Kutsen Kasar Rasha a cikin kasashen Sahel

Hoto: Sam Mednick/AP/dpa/picture alliance

 Sabon yunkuri na kutse a yankin Sahel din da kasashen duniya ke yi, a kokari na nuna karfin ikon a tasiri tsakanin Amurka, Rasha da China, inda Rashan ke son ture tsohon kawancen da kasashen Turai ke da shi da kasashen yankin musamman Jamhuriyar Nija rya yi tasiri sosai a kan halin da ake ciki a yanzu. To sai dai ga Farfesa Hussani Tukur masanin siyasar kasa da kasa da ke jami’ar jihar Nasarwa na mai bayyana cewa.

Barazanar durkushewar ECOWAS

Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Tun kafin kai wa ga wannan hali na tsaka mai wuya ake yiwa kungiyar ta Ecowas kalon wacce tasirinta ke raguwa, domin ko ta yi ihu baya yin tasiri. Allal misa kotun da kungiyar ta kafa ta kan yanke  hukunce-hukuncene na jeka na hika, domin mafi yawan kasashen kungiyar ba sa aiki da hukuncin, abin da ya sanya ta zama tamkar magen lami ba ki cizo baki ya kushi. Kwararru na bayyana bukatar kungiyar Ecowas din ta yi taka tsan-tsan da barazanar da ke fuskanta a wannan rikici na cikin gida. Domin sauran kara fadada kungiyoyin yankinsu suke da ma hada kai ta hanyar kawar da shingaye da ma  hadewar tattalin arziki da al’adu, inda duniyar ke kara zama dan  karamin kauye.