1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ke gaban Harris na yin nasara a zaben Amurka

August 23, 2024

Kamala Harris ta yi jawabin karbar takarar shugabancin Amurka a karshin jam'iyyar Demokrats, kasa da kwanaki 80 kafin babban zaben watan Nuwamba.

Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Cikin kazar-kazar da farin-ciki da fara'a da yin godiya ta musanaman ga Shugaba Biden, Kamala Harris ta bada takaitaccen tarihinta a matsayinta na tsatson Indiyawa ta wajen uwa, bakar fatar Jamaica ta bangaren Uba, amma kuma haifaffiyar Amurka. Daga nan sai ta ce "A madadin dukkan Amurkawa ba tare da la'akari da jamIyya  ko launin fata ko jinsi ba, na karbi wannan takara da kuka ba ni".

Ganin cewa akasarin Amurikawa ba su san ta ba sosai, Kamala ta yi amfani da damar wajen kwatanta kanta na tsohuwar Mai shari'a, mai aiki da doka da Donald Trump, tsohon mai laifi. Ta nuna  cancantarta fiye da Trump da hatsarin sake zabarsa, cewa ya tanadi munanan manufofi da ba za su yi wa kasar nan alheri ba, musanman wajen kassara ayyukan jin dadin Iyali, nakasa asusun gata da hana majalisa ta yi aikin da ya dace wajen magance matsalar baki 'yan ci cirani.

Hoto: J. Scott Applewhite/AP Photo/picture alliance

'Yar takarar ta Demokrats ta bai wa Amurkawa tabbacin kyakykyawan dorewar ci gaba idan suka ba ta amanar jan alakar kasar. Kamala ta ci alwashin saukaka bukatun rayuwar yau da kullum, rage karancin muhalli, inganta kiwon lafiya da samar da karin ayyuka. Da ta juya ga batun kasashen waje, kusan babu wani abu sabon abu game da abinda aka saba ji kan rikicin Falasdinawa da Isra'ila, cewa suna kokarin samun tsagaita wuta, Falasdinawa su zauna cikin martaba, amma tare da nanata aniyar gwamnatin Amurka ta ci gaba da marawa Isra'ila baya.

Hoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Kamala, ta yi ahir ga kasashe irin su Iran da Koriya ta Arewa, tare da bada tabbacin cewa gwamnatinta za ta cigaba da huldar arziki da kawayen Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, sabanin Donald Trump mai rusa zumunci, amma yake haba-haba da masu kama-karya irin shugaban Rasha da na Koriya ta Arewa.

Manyan kalubalen da ke gaban Kamala a halin yanzu, sun hada da yadda za ta tsaya da kafafunta, ta fayyace bambamcin manufofinta da na Shugaba Biden, saboda rashin yin hakan zai sa wasu su ga kamar Biden ne zai cigaba da mulki. Akwai kuma bukatar ta dukufa neman amincewar Turawan yankunan karkara musanman a jihohin raba-gardama, saboda a nan ne Donald Trump yake da masu tula masa kuri'a na amana, wadanda har yanzu suna tare da shi.

Ya kuma zama wajibi, Kamala Harris ta fara ganawa da 'yan jarida sosai, wanda hakan zai magance gorin da 'yan adawa suke yi mata cewa tana dari-darin amsa tambayoyin ba-zata.