1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ke tattare da zaben majalisun dokoki a Kenya

March 1, 2013

Duk da gamsuwar da masu sanya ido suka yi game da shirye-shiryen zabe a Kenya, akwai matsalolin da wasu ke gani ka iya tasowa.

Kenyan voters nominate people for political positions including those of MPs, governors and senators. Foto: Alfred Kiti, Nairobi, Kenia vom 17.01.2013
Hoto: DW

Ko wane dan Kenya yana da kuri'unsa shidda ne da zai kada a zaben na ranarLitinin. Hakan zai baiwa yan kasar damar zaben sabbin hukumomi masu yawa da za su taimaka domin kara maida kasarsu kan tafarkin demokradiyya da daidaituwa a rayuwar yau da kullum. Ko wace gunduma za ta kasance tana da mai wakiltar al'amuran mata a sabuwar majalisar dokokin da za'a zaba. Gwamnatoci na kananan hukumomin 47 da ake dasu a Kenya din nan gaba za su rika samun damar yanke kudirori kan abubuwan da suka shafe su da kansu, ba sai sun jira gwamnatin tsakiya a Nairobi ta yanke masu shawara ba. Yan Kenya za su kuma zabi sabuwar majalisar dattijai, wadda a birnin Nairobi, za ta taimaka domin ganin yankunan karkara na jihohin kasar ta Kenya sun kara samun karfin fadi aji a siyasar kasar baki daya. Masanin al'amuran siyasa a Nairobi, Nyaigoti Chacha yace yana fatan zaben zai haifar da canje-canje masu yawa a wannan kasa, saboda:

"Akwai canje-canje masu yawa da kuma kula da aiyukan juna da za'a samu nan gaba, saboda kasancewar za mu sami majalisun dokoki guda biyu da kuma gwamnatin da za'a rage karfin ikonta zuwa jihohi da larduna, wadanda za su zura ido, su kuma matsa lambar ganin wakilansu a majalisun dokokin guda biyu sun aikinsu a can sosai.

Abokan kawancen Raila Odinga a zaben KenyaHoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

'Yan takarar da ke sahun farko a zaben Kenya

A karkashin sabon tsarin, za'a rage karfin ikon shi kansa shugaban kasa. Takarar neman wannan mukami yanzu haka dai ta fi karfi ne tsakanin mutane iyu. Sauran yan takara shidda dake neman mukamin na shugaban kasa ra'ayoyi sun nuna ba za su kai ko ina ba. Bincike ya nuna cewar dan takarar dake kan gaba shine Raila Odinga, ko da shike haka ma al'amarin ya kasance shekaru biyarda suka wuce, inda akai yi tsammanin shi zai lashe zaben, amma ya sha a hannun shugaba mai ci Mwayi Kibaki. Bayan tashin hankali da zubar da jini na watanni biyu tsakanin magoya bayan 'yan takarar biyu, Kibaki da Odinga sun daidaita a game da kafa gwamnatin hadin kan kasa inda Odinga ya zama firayi minista.

Abokin takarar Odinga a wannan karo ma ya fito ne daga kabilar Kikuyu: wato Uhuru Kenyatta, dan shugaban farko na Kenya. To sai dai dan takarar yafi daukar hankali ne sakamakon tuhumar dake kansa a kotun kasa da kasa dake birnin Hague, dake neman sa da laifin aikata kisan gilla na ramuwa kan 'yan kabilar Kalenjin da Luo. Yanzu kuma sai gashi Kenyatta ya hada kansa da dan kabilar Kalenjin, William Ruto domin neman cimma burinsu, ko da shike shima kotun kasa da kasar tana tuhumarsa da laifin kisan kare dangi.

Joaquim Chissano, tsohon shugaban MosambikHoto: Johannes Beck

Gamsuwa da shirye-shiryen zaben Kenya

A halin da ake ciki kuma, hukumar zabe ta Kenya tana kokarin ganin ba'a yi zaben tare da magudi ko almundahana ba, yadda zargin aikata rashin gaskiya ba zai yi jagora ga tashin hankali da zub da jini kamar yadda ya faru shekaru biyar da suka wuce ba. Duk da kura-kurai, musamman a game da rajistar masu zabe, amma hukumar ta sami goyon baya a aiyukanta daga masu lura da zabe na kasa da kasa. Tsohon shgaban Mozambique Joachim Chissano shine jagoran tawagar yan kalo ta kungiyar hadin kan Afrika.

Muna da ra'ayin cewar mun sami cikakken bayani daga mutanen da suka kware kan aikinsu, wadanda kuma suka shirya sosai domin tafiyar da wannan aiki. Wannan kuwa ya sanya mana karfin zuciyar cewar zaben za'a gudanar dashi sosai yadda ya kamata.

Sai dai kuma ganin ko wane dan Kenya yana da kuri'unsa shidda ne a lokacin zaben, ana bukatar fasaha mai tsanani a kasar da bata da tabbas a game da samun wadataccen karfin lantarki.

Mawallafi : Umaru Aliyu
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani