Najeriya: Janye tallafin AIDs ko SIDA
September 9, 2019Najeriyar dai na daga cikin kasashen da suka ga haske a yakin da suke da kwayar cutar ta HIV AIDs ko SIDA da ke karya garkuwar jiki a 'yan shekarun nan, domin yawan mutanen da ke dauke da kwayar cutar ta HIV AIDs ko SIDA ya ragu daga miliyan uku zuwa milyan daya da dubu 800. Wannan nasara dai ta faru ne, biyo bayan kara kaimi wajen yakar cutar tun daga shekara ta 2015. To sai dai hasken na neman komawa duhu a yanzu, sakamakon fara janye tallafi da kasashen duniya suka yi, domin a cewarsu Najeriyar ta na da kudin da za ta iya rike kanta. Su kansu kungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafawa masu fama da cutar HIV AIDs ko SIDA a Najeriya sun fara kokawa.
Rahin zuwa gwaji: Kalubalen yaki da cutar
Abin da yafi daga hankali shi ne har yanzu akwai mutanen da ke tsoron fitowa a gwadasu domin sanin ko suna dauke da cutar. Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin mutane miliyan daya da dubu 800 da ke fama da cutar, mutane miliyan daya da dubu 500 ne kawai ke karbar magani. To sai dai babban daraktan hukumar yaki da kwayar cutar HIV AIDs din ko kuma SIDA, Dr Gambo Aliyu y ace suna tsara yadda zasu shawo kan wannan kalubale. Tuni dai majalisar wakilan Najeriyar ta bayyana kara kaimi na tabbatar da samun kudin da za a rinka kulawa da masu cutar. Abin jira a gani shi ne sabuwar dabarar da Najeriyar za ta bullo da ita, wajen samar da kudin a cikin gida, domin kaucewa dogaro da samun tallafin da ba zai dore ba.