1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen samar da sabon kundin tsarin mulki a Libiya

February 19, 2014

A wannan Alhamis din ce 'yan kasar Libiya za su zabi wakilan kwamitin da zai rubuta kundin tsarin mulkin kasar mai mutun 60, inda ko wace jiha za ta bayar da mutun ashirin.

Libyen Stammesfehden vor den Toren Tripolis
Hoto: DW/V. Stöcker

Sai dai tuni ake ganin cewa, wannan Kwamiti idan ya hadu, to yana da babban nauyi a kan sa na gabatar ma yan kasar ta Libiya sabon kundin tsarin mulki nan da sabon wata mai zuwa. Yayin da zaben dake karatowa a wannan kasa ke nuna halin rashin tabbas.

'Yanzu dai ta tabbata cewa zaben membobin Kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin kasar Libiya, zai gudana ne a ran ashirin ga wannan watan nan na Febrairu.Tun karon farko dai an tsaida cewa za'ayi wannan zabe a watan Nuwamba na 2013 amma aka dage shi sabili da rashin cikakken tsari. A zaben da aka yi na 'yan majalisun dokokin kasar na watan Yuli 2012 kusan rabin al'ummar kasar basu samu yin rajista ba.

Sannan kuma wata babbar matsalar ita ce, 'yan kabilar Amazig makiyaya dake arewa maso yammacin kasar ta Libiya, sun ce ba za su tsayar da 'yan takara ba, duk kuwa da cewa an tanadar musu kujeru biyu. Inda suka tsaya kan cewa, sai fa an rubuta batun 'yancin su cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Hoto: picture-alliance/dpa

Maurad Blal, wanda ke daya daga cikin 'yan takara na Kwamitin mutanen Sittin masu rubuta kundin tsarin mulkin, dake mazabar Tripoli wanda kuma ke aure da mata yar kabilar Amazig, bai ji dadin daukan wannan mataki na kauracewar da yan wannan kabila suka yi ba.

Ya ce: Ina da abokai da dama 'yan kabilar Amazig, a ganina wannan kuskure ne, ya kyautu su bada 'yan takara ga wannan kwamiti na mutun sittin.

Ana ci gaba da cece kuce kan batun ka'idodin tsayar da 'yan takarar wanda bai tilasta cewa sai mai wata takardar shaidar karatu haka ko haka zai tsaya ba.

Mohamed Tumi, shi kuma lauya ne, kuma yana fatan cewa sanin da yake da shi a fannin shari'a zai taimaka a zabe shi, kuma a ganin shi kasancewar mutane masu sani daban daban cikin wannan kwamiti ba zai zamo wata matsala ba.

Hoto: Reuters


Ya ce: Bai zama dole ba sai mutanan sittin sun kasance masana doka, ko dokokin tsarin mulki ba.

Kundin dokoki, ya bada izinin daukan wasu mutane na daban, ko kuma ma'aikatan kasa da kasa, ko ma wasu manyan masana dokokin tsarin mulki duk suna iya bada tasu gudun muwa.


Lubna Muntasser mai koyar da harshen Englishi ce, kuma bata da isheshen sani kan harkokin shari'a, amma hakan bai hana wannan yar takara yin nazari kan kasancewar kundin tsarin mulkin da za'a zaba nan gaba ba.


Ta ce: Ina kara nanatawa, kuma ina kira a gaskiya,da a fitar da kundin tsarin mulki mai haske, bama bukatar dunkulallun bayannai, wanda da kowa zai fasara yadda take gyarashi ba, in so samu ne, kamar musalin kundin tsarin mulkin kasar Tunusiya, kuma na kasar Masar ma ya bani sha'awa.

Majalisar dokokin kasar ta Libiya, na tsammanin cewa za'a amince da kundin tsarin mulkin ta hanyar zaben raba gardama nan da karshen bazara, sannan sauran zabubukan kasar su biyo baya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar