Tattalin arziki
Matsalolin tattalin arziki a Libiya
February 15, 2020Talla
Gwamnatin da Majalisar Dinkin dunya ta amince da ita a kasar Libya karkashin ikon firaminisra Fayez al-Sarraj ta bayyana cewar kasar za ta fuskanci kalubale a kasafin kudi wanda zai haifar sakamakon toshe cibiyoyin hakar mai da mabiya kwamanda Khalifa Haftar suka yi a kasar.
Hasashen ya biyo bayan kiraye-kirayen da masu shiga tsakanin a rikicin kasar suke yi wa 'yan tawayen da ke gabashin kasar kan muhimmancin sulhu domin Libiya ta farfado daga rikicin da ta afka tun bayan mutuwar Marigayi Shugaba Moammar Ghaddafi.