1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maita: Azabtar da wadanda ake zargi

August 11, 2020

Kasashen duniya da dama sun jima da jinge batun nan na maita, sai dai lamarin ya sha bamban a wasu kasashen, inda mata da yawa da ake zargin mayu ne ke ci gaba da fuskantar kalubale iri-iri.

Symbolbild Afrika Hexenverfolgung
Yadda ake jan wata mata da aka ce mayya ce, zuwa wajen da za a zartar mata da hukunci a MuzambikHoto: picture-alliance/Design Pics/K. Welsh

Irin wannan hali da mayu kan tsinci kansu ne dai ya sanya ake yaki da muzguna musu a duniya. Mayu da dama dai kan fuskanci tsangwama daga al'ummar yankunan da suka zaune, yayin da wasunsu kan rasa rayukansu musaman ma idan aka zarge su da kama wani ko da kuma lamarin ba haka yake ba. Masu rajin kare hakkin dan Adam a sassan duniya dabam-dabam, na ci gaba da yin kira ga jama'a da kuma mahukunta domin kawo karshen yadda ake muzgunawa mutanen da ake zargin su da maita.

Fafutuka daga Coci

Cocin mabiya darikar Katolika ma na fafutuka wajen kwatar wa irin wadannan mutane hakkinsu. Wannan aiki kuwa na karkashin wani shiri ne da ke samun kulawar shugaban darikar ta Katolika na duniya da kansa.

An jima ana muzgunawa wadanda ake zargi da maita Hoto: picture-alliance/akg-images

A baya dai Cocin ta Katolika na goyon bayan wannan sabga ta maita musamman ma a nahiyar Turai, amma fa bisa ga irin bayanan da masana tarihi suka fidda, mayu da yawansu ya kai dubu 50 zuwa 60 ne suka rasa rayukansu tsakanin karni na 15 zuwa na 18. Sai dai a wannan zamanin an samu sauyi kan batun, amma kuma a nahiyar Afirka lamarin ya sha bamban, domin kuwa jama'a da dama na ci gaba da kashe mayu da kuma tauye musu hakki. 

Farfesa Wolfgang Behringer, masanin tarihi a Jami'ar Saarland da ke Jamus ya shaidawa tashar DW irin rawar da suke takawa: "A kasashen da muka tallafawa kungiyoyi da ke aiki kan wannan batu, mun fuskanci akwai matsaloli na tauye hakkin mayu da nuna musu wariya, kuma wannan kyama da muzgunawa fa, ba wai mata kadai ake yi wa ba, har ma da maza da kuma yara kanana."

Kananan yara ma ba su tsira ba

Wannan batu da Mr. Behringer ke magana na sanya yara cikin wadanda ake zargi da maita kusan abu ne da ke kokarin zama ruwan dare a kasashe irinsu Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, musamman ma dai yaran da aka haifa da nakasa.

Wuri na musamman da ake tsare da wadanda ake zargi da maita. a gidan yarin mata na Bimbo da ke Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Getty Images/AFP/F. Vergnes

Jama'a kan kaurace wa irin wadannan yara, inda mafi akasari suke rayuwa su kadai cikin yanayi na galabaita, kamar yadda Therese Mema Mapenzi da ke cikin masu fafutuka wajen bada tallafi da kuma kwato hakkin irin wadannan yara ta bayyana a zantawarta da DW, inda ta ce sun yi rijistar yara da dama da aka zarga da maitar. 

Irin wannan yanayi da ake ciki na muzgunawa da ma kashe wadanda ake zargi da maita ne ya sanya mutane irins Theresa Mema da sauran masu fafutuka, yin kiran da a yi zama na musamman a yankunan da ake da irin wadannan matsalolin domin kawo karshen halin da mayu kan shiga. Daya daga cikin abin da kuma Theresa ke son ganin an mayar da hankali a kai shi ne, dinke barakar da ke akwai tsakanin iyalan da batun na maita ya farraka, sannan kuma a ci gaba da fadakar da mutane a fadin duniya kan illar da ke tattare da daukar doka a hannu a kan wadanda ake zargi da maitar.