Kalubalen 'yan gudun hijirar Sudan a Uganda
February 11, 2026
Dubban 'yan kasar Sudan da suka guje wa yaki a kasarsu a 'yan shekarun da suka gabata, kuma da dama daga cikinsu sun shiga kasar Uganda ne tare da iyalansu domin samun mafaka. Sai dai duk da mafakar da suka samu, da dama na fuskantar kalubale ta fannoni da dama ciki har da na kiwon lafiya.
Karancin kudin kashewa saboda rashin aikin yi da 'yan gudun hijirar ke fama da shi da kuma rashin iya Turancin Ingilishi wanda shi aka fi yi a Uganda ya sanya mafi akasarin 'yan gudun hijira kasa zuwa asibitoci domin duba lafiyarsu. Wannan yanayi da suka shiga ya sanya wasu daga cikin likitocin da aka yi gudun hijirar da su yanke shawarar kafa asibiti kuma sun yi hakan ne ta hanyar sayen wani tsohon asibiti a lardin Kabalagala da ke birnin Kampala, kamar yadda Dr. Assadiq Ibrahim da ya jagoranci kafa asibitin ya shaida wa DW.
Mu uku ne muka hadu muka kafa asibitin. A baya kowannenmu na da asibitin kansa a Sudan amma da muka yi gudun hijira sai ya kasance ba mu da aiki, sai daga baya muka yanke shawarwar hada gwiwa wajen kafa asibiti domin mun iske 'yan Sudan da dama ba su iya Turanci da sauran yaruka da 'yan Uganda ke yi ba kasancewar a gida Sudan Larabci kawai ake yi.
Makonni kalilan bayan fara wannan aiki da Dr. Ibrahim da takwarorinsa suka yi, asibitin nasu ya fara samun karbuwa, inda suke ganin marasa lafiya 'yan Sudan kyauta sannan suka ware wasu ranakun don kula da lafiyar wadanda ke da kudin da za su iya biya don a duba lafiyarsu. Mafi akasarin 'yan Sudan din da ke zuwa asibitin dai sun raunata ne sakamakon yaki, yayin da wasunsu kan je da wasu cutukan ciki kuwa har da na hakori wanda Dr. Shimaa Mahmoud da ke cikin wanda suka kafa wannan asibiti ta ce shi ma yana da nasaba da yakin.
Ka san yadda tashin hakali yake, yana shafar lafiyar hakori. Dadashin mutum kan samu matsala sosai saboda rashin kula da shi da kuma rashin shan ruwa mai tsafta. Wannan na shafar lafiyar hakora sosai. Har wa yau wanda ke cikin damuwa na iya tauna hakoransa musamman da dare saboda irin yanayin damuwar da suka shiga.
Yayin da wadannan likitoci ke ci gaba da bayar da tallafi ta fuskar kiwon lafiya ga 'yan uwansu 'yan gudun hijira, a share guda likitocin da 'yan uwansu 'yan Sudan din na fatan samun zaman lafiya mai dorewa a kasarsu don su samu su koma gida da nufin ci gaba da yin irin rayuwar da suka saba kafin kasarsu ta afka cikin yanayin yaki.