Kama sojojin ruwan Rasha a Lagos
October 23, 2012Hukumomin Tarayyar Najeriya sun cafke wasu 'yan Rasha 15 bayan da suka gano makamai masu tarin yawa da kuma albarusai 8500 a jirgin ruwan da ke dauke da su. Kakakin rundunar sojojin ruwan Najeriya Commodore Aliyu Kabiru ya ce tun a karshen mako ne suka yi nasarar bankodo sirri jirgin ruwan na Moscow a gabar ruwan Lagos. Wata majiya da bato so a bayyana sunanta ba ta ce daga cikin makamai da a gano har da bindigo da ke sarrafa kansu da kansu.
Fashin teku da safarar miyagun makamai na dada samun gindin zama a ruwan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro da kuma fashe fashen bututan mai a yankin Niger Delta. 'Yan fashi na amfani da tekun Lagos wajen jigilar makamai ba bisa ka'idama zuwa wasu sassa na yammacin Afirka da ma dai duniya baki daya.
A shekara ta 2010 ma dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Tarayyar ta Najeriya da Iran bayan da ta gano makaman da aka zargi hukumomin Teheran ke kai wa 'yan tawayen Casamance na kasar Senegal.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu