1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamala Harris ta kamu da cutar Covid-19

Mouhamadou Awal Balarabe
April 26, 2022

Gwajin corona da mataimakiyar shugaban Amirka Kamala Harris ta yi ya tabbatar da cewa ta kamu da cutar. Ana samun karuwar wadanda suka kamu da corona a Amirka sakamakon yaduwar nau'in BA.2 na Omicron.

USA | US-Vizepräsidentin Kamala Harris
Hoto: Evelyn Hockstein/Pool Photo via AP/picture alliance

Sanarwar da kakakinta Kirsten Allen ta fitar ta nunar da cewa Kamala Harris ba ta da fama da zafin jiki, amma ta kebe kanta sakamakon kamuwa da corona, kuma za ta ci gaba da aiki daga gida.

Ba Misis Harris ba ce babbar jami'ar gwamnatin Biden ta farko da ta kamu da covid-19 ba. Ko da ministan Shari'a, da mai magana da yawun shugaban kasar Jen Psaki ko kuma kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi sun kamu da kwayar cutar a cikin 'yan makonnin da suka gabata

Sai dai Shugaba Biden mai shekaru 79 wanda ya karbi allurar rigakafin cutar ta Covid sau biyu, ba ya cikin rukunin wadanda suka yi ma'amala da Kamala Harris a baya bayannan, kamar yadda hukumomin lafiya na Amirka suka bayyana. Ana samun karuwar wadanda suka kamu da corona a Amirka sakamakon yaduwar nau'in BA.2 na Omicron.