1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Joe Biden ya mika ragama wa Kamala Harris

Abdourahamane Hassane
August 20, 2024

Shugaban Amirka Joe Biden ya yi jawabin bankwana a wajen babban taron jam'iyyar Democrat a birnin Chicago, inda ya mika ragamar neman takarar shugabancin kasar na jami'iyyar ga Kamala Harris.

Hoto: J. Scott Applewhite/AP Photo/picture alliance

Shugaban wanda ya yi jawabi a gaban daruruwan jama'ar da suka rika yi masa tabi da shewa, ya ce zai taya Kamala yakin neman zaben. ''Amirkawa  ina sonku, shin kun shirya damara tabbatar da demokaradiyya, ina tambayarku, kun shirya tabbatar da ganin nasara kamala Harris tare da goyon bayanku.''

A wajen taron, mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris ta rika zubar da hawaye a yayin jawabin shugaban. Joe Biden dai ya sallama ga yin takarar saboda yawan shekaru sakamakon matsin lamba da ya fuskanta daga 'ya'yan jam'iyyar ta Democrat.