1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Kamaru sun ja kunnen 'yan adawa a kasar

September 21, 2020

Gwamnatin Kamaru ta fidda sanarwar haramta duk wata zanga-zanga a kasar. Sanarwar da ministan harkokin cikin gida ya fitar ta ce an tanadi jami’an tsaro don zama cikin shiri.

Kamerun Maurice Kamto Oppositionspolitiker
Hoto: Gety Images/AFP/S. De Sakutin


Gamayyara jam’iyyun adawan kasar Kamaru karkashin jagorancin madugun adawa Maurice Kamto sun sha alwashin kawo karshen mulkin Shugaba Paul Biya na sama da shekaru 38.

Kamto da magoya bayansa sun shirya kaddamar da wata gagarumar zanga-zanga da tuni ake kwatantawa da irin wanda ya samar da juyin mulki a kasar Mali.


Wannan shi ne karon farko da mulkin Shugaba Paul  Biya ke fuskanta barazana daga bangaren adawa, wanda tuni masana ke ganin akwai bukatar a dauki mataki don gudun aukuwar abin da ya faru a Mali. 

A gobe Talata (22.09.2020) ne aka shirya gudanar da zanga-zangar.