1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Haramta tallan abinicn jarirai a Kamaru

Zakari Sadou LMJ
August 1, 2023

Ministan lafiya a kasar Kamaru Manaouda Malachie ya haramta tallata abincin jarirai da kamfanoni ke sarrafawa a asibitocin kasar, sakamakon gaggarumin koma-baya da ake samu wajen shayar da yara nonon uwa.

Kamaru | Haramci | Talla | Abincin Jarirai | Muhimmanci | Nono Uwa | Shayarwa
Haramta tallata abincin jarirai domin karfafa shayar da nonon uwa a KamaruHoto: dapd

Matakin haramta tallata abincin jariran kamfanoni ke sarrafawar da ministan lafiyar Kamarun Manaouda Malachie ya dauka na zuwa ne daidai lokacin da ake bikin ranar shayar da nonon uwa ta duniya, inda hukumomin kasar za su kwashe mako guda na fadakar da uwaye mata muhimmancin shayar da yara nonon uwa zalla maimakon abincin yara da kamfanoni ke sarrafawa. A cewar hukumomin, yara uku ne daga cikin 10 kacal ake shayarwa nonon uwa, abin da ke nuna gagarumin koma-baya a kokarin karfafa shayarwa musamman a watanni shida zuwa 12 na farkon rayuwar yaro.

Masana na cewa jariran da aka shayar nonon uwa sun fi samun lafiya da kumariHoto: AP

Masu rajin tabbatar da shayar da yara nonon uwa kamar Ngo sak Cécile Patricia sun nunar da cewa, shayar da jariri nonon uwa yafi gina jiki da shayar da su madara. Akwai dai iyayen da har yanzu ba su yarda da shayar da jarirai nonon uwa zalla ba, saboda suna ganin hakan ya kan jawo wa yaran matsala. Wasu iyayen kuma na yaye 'ya'yansu domin suna gudun kar su cutar da yaran ta hanyar ba su nonon sakamakon cututtukan da suke dauke da su, abin da ya sanya likitocin yara nuna damuwa ganin yadda wasu kamfanonin sarrafa abincin yara suke amfani da wannan damar wajen sayar da kayayyakinsu. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci gwamnatocin kasashe, su bayar da gudunmawa domin cimma burin da aka sa a gaba.