1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Gyaran kundin zabe ne mafita a Kamaru?

Fotso Henri AH/LMJ
November 12, 2025

Yayin da ya fara sabon wa'adin shekaru bakwai a matsayin shugaban kasar Kamaru, Shugaba Paul Biya ya tattauna game da yiwuwar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki.

Kamaru | Shugaban Kasa | Paul Biya | Gyara | Kundin Zabe | Kundin Tsarin Mulki | Adawa | Issa Tchiroma Bakary | Dimukuradiyya
Wa'adi na takwas na tsawon shekaru bakwai, yaushe Shugaba Paul Biya zai sauka?Hoto: Angel Ngwe/AP Photo/picture alliance

Gyaran kundin tsarin zabe, na iya bayar da damar samun mukamin mataimakin shugaban kasa. Wannan furci na shugaban kasar Kamaru Paul Biya na zuwa ne, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabukan 'yan majalisu a shekara mai kamawa.

Bukatar kawo gyara

Shugaba Biya ya fara tunanin kawo sauye-sauye a fuskar siyasar kasar, kwanaki kalilan bayan rantsar da shi. Tun da fari a cikin jawabinsa na karbar mulkin, ya yi shelar yin kwaskwarima ga kundin zabe. "Ya kamata mu mika bukatar yin wasu gyare-gyare ga majalisar dokoki, wadanda za su bayar da damar inganta aikin gwamnati......." A cewar Biya.

Karin Bayani: Hanyar kauce wa rikicin bayan zabe a Kamaru

Manazarta a kasar ta Kamaru na ganin cewa, sauye-sauyen da shugaban zai kawo za su karfafa dimukuradiyya. Amma a bangare guda ana ganin wata hanya ce ta kara kautar da 'yan adawa daga mulki, duk da cewar jagoran adawar da ya sha kaye Issa Tchiroma Bakary har yanzu yana ganin yana iya  ja da gwamnatin da ya ce ta yi kwacen zabe.

Hoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

Farfesa Louisson Essomba mai yin sharhi ne  a kan al amamuran siyasa: "Hakika a cikin wannan tsarin za mu iya ganin cewa shugaban na Kamaru yana son ya tafi da zamani a cikin tsarin mulkin, musamma na kirkirar mukami na mataimakin shugaban kasa................."

Murkushe 'yan adawa ko bayar da kai....?

Gyaran fuskar zai shafi kudin tsarin mulki da kudin zabe da hukumar zabe. Amma abin da ya fi muhimmanci ga 'yan adawa a cikin watanni masu zuwa shi ne, zaben 'yan majalisu da na kananan hukumomi da ake sa ran za a yi a cikin watan Mayu na shekara ta 2026 da ke tafe.

Kwanaki uku bayan bikin rantsar da Paul Biya, jagoran adawa Tchiroma Bakary ya bayar da wa'adin sa'oi 48 ga hukumomi a Yaoundé da su saki dukkan wadanda suka kama. Ga dukkan alamu hukumomin sun ba da kai bori ya hau, saboda sun fara sako fursunonin siyasar da nufin kwantar da wutar rikici a kasar.