1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mata na yajin cin abinci don neman zaman lafiya

Abdul-raheem Hassan RGB
May 20, 2021

Dubban mata a Kamaru sun shiga wani yajin cin abinci da zummar jan hankulan manyan kasashen duniya kan kawo doki a rikicin yankin masu magana da Turancin Ingilishi.

Coronavirus | Südafrika Kapstadt | Warten auf staatliche Zuschüsse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. Engelbrecht

Matan na Kamaru sun shiga yajin kin cin abinci don jan hankalin manyan kasashen duniya don kawo musu doki kan rikicin yankin kasar na masu magana da Turancin Ingilishi da ya shiga shekara ta biyar. Rikicin da yayi sanadiyar rayuka da dama da tilasta wa wasu miliyoyi gudun hijira. Wadannan matan na gudanar da zanga-zangar a kan titunan Kamaru da zimmar matsawa gwamnati kawo mafita kan rikicin yankin masu magana da harshen Turanci Ingilishi a kasar.

Karin Bayani:  Mata na fiskantar cin zarafi a duniya

Sai dai wannan yunkuri ya gaza cimma nasara, wannan ya sa matan suka sauya salo, inda dubbai daga cikinsu suka ja daga na shiga yajin cin abinci har sai hakarsu ta cimma ruwa. Wadannan mata sun ce ba gudu ba ja da baya a ci gaba da sawa bakinsu takunkumi da cimaka, a cewarsu, za su ci gaba da zama da yunwa har sai bukatarsu ta biya.

Karin Bayani:  Shirin zaman lafiya a Kamaru ya faskara

Baya ga neman kawar da rikicin yankin Ambazoniya, akwai tarin matsaloli da ke damun matan, kamar fyade da kisan gilla da kuma garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Gwamnatin Shugaba Joe Biden a Amirka ta nuna alamun shiga maganar, inda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya ce lokaci ya yi da Washington za taka rawa a rikicin na Kamaru. Yanzu haka dai kusan shekaru biyar kenan ake gwabza fada, inda aka yi asarar rayuwa akalla 3,500 sama da mutane miliyan daya sun tsere zuwa hijira.