1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwararrun ma'aikata na tserewa daga Kamaru zuwa Turai

February 22, 2024

A kasashe masu tasowa akasarin matasa da kwararrun ma'aikata na tserewa zuwa kasashen ketare, domin samun aikin yi da kuma albashi mai tsoka. Kasar Kamaru, na daga cikin irin wadannan kasashe.

Paul Biya | Kamaru8 | Kwararru | Tserewa | Tsadar Rayuwa
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

To sai dai sannu a hankali gwamnatin Yawunde ta fara yin kira ga kwarraru 'yan kasar da su nuna juriya su ci gaba da aiki a kasarsu ta hauihuwa, kasancewar Kamarun na zaman guda cikin kasashen da 'ya'yanta ke yin fice a fannoni na dama a wasu kasashen musamman kasashen Yamma. Yawan ficewar 'yan kasar kuwa ba wai saboda rikicin tawayen Ambazoniya ne kawai ba, har ma da rashin albashi mai tsoka da kuma gwamnatin da ake ganin ta gaza a fannoni da dama na kula da al'ummarta. Shugaba Paul Biya ya bayyana cewa burin kwararrun matasan kasar na ficewa zuwa ketare ya zama babban abun damuwa, musamman idan aka ga har da kwararrun da yanzu haka ke rike da guraben aiki a kasar. Sai dai wata malamar makarantar ta shaidawa DW cewa, ba za ta bai wa matasa shawarar su amince da kalaman na Paul Biya ba. A cewarta ita kanta a yanzu tana neman takardun ficewa daga Kamarun zuwa kasar Kanada ta halastacciyar hanya.

Kamaru: Matashi mai neman aikin yi ga matasa ta yanar gizo

03:10

This browser does not support the video element.

Idan dai ana son magance matsalar ficewar kwararru to dole gwamnatin Kamaru ta dauki matakan sharewa ma'aikata hawaye wajen biyansu albashi mai tsoka, a cewar masanin kan harkokin shige da fice na kasa da kasa Tumenta Kennedy. Kasar ta Kamaru dai na yin asarar dubban kwararrun malaman jinya da likitoci da malaman makarantu da jami'o'i, wadanda ke barin kasar zuwa kasashen waje domin samun rayuwa mai inganci. Koda a bara ma hukumomin kasar ta Kamaru sun ce yawan 'yan kasar da suka nemi takardun kaura zuwa Amurka da Kanada ya karu da kaso 70 cikin 100, abin da ke zama babbar barazana ga makomar kasar. A yunkurin magance matsalar gwamnatin Kamaru ta sanar da bai wa 'yan kasar dalar Amurka 4000 da kuma dauke haraji ga duk wani dan kasuwa dan kasar, wanda ya amince ya koma gida ya ci gaba da kasuwancinsa. Haka kuma gwanatin ta ja hankali 'yan kasar da su rungumi noma, maimakon ficewa daga kasar domin samun rayuwa mai inganci.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani