1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta haye mataki na gaba a gasar AFCON

Mouhamadou Awal Balarabe ZMA
January 5, 2026

Tunisiya da ake ji da ita ta yi abin fallasa a yayin da Kamaru ta bada mamaki inda ta haye mataki na gaba na gasar AFCON.

Kamerun Douala 2022 | Massadio Haïdara bejubelt sein Tor für Mali beim Afrika-Cup gegen Mauretanien
Hoto: Alain Guy Suffo/Sports Inc/empics/picture alliance

A gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka da ke gudana a Maroko, an yi wasanni hudu na zagaye na biyu, inda a jiya Lahadi da kyar Maroko mai masaukin baki ta yi nasara doke Tanzaniya da ci daya mai ban haushi. Hasali ma dai, Maroko ta fuskanci turjiya daga Tanzaniya a mintuna 60 na farkon wasan, kafin ta dogara kan zakakurin dan wasanta Brahim Diaz wajen zura kwallo a minti na 64, lamarin da ya ce ta daga tarnakin abokiyar hamayya. Amma kocin Lions da l' Atlas ta Maroko Walid Regragui ya ce da kyar na tsira ya fi da kyar aka kama ni.

"Mun san cewar wasan ba zai yi mana sauki ba, duk da cewa ba mu yi tunanin cewar zai kai wannan matsayi ba a yau. Sai bayan da aka dawo hutun rabin lokaci muka fara nuna kuzari. Mun tafka kurakurai da yawa a matakin farko, inda aka samu da rashin kokari na 'yan wasa, tare da ba wa abokan hamayya kwarin gwiwa a damarmaki biyu ko uku da suka samu. Amma abin farin ciki shi ne, mun gyara kurakuranmu bayan da aka dawo hutun rabin lokaci. Kamar yadda na saba fada a irin wannan gasa, abu mafi mahimmanci shi ne a tinkara wasa yadda ya kamata. Idan da a da ne, da mun sha kashi, amma a yau mun cancanci zuwa zagaye na gaba, kuma wannan shi ne abin da ya fi muhimmanci".

Hoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto/picture alliance

Ita dai Maroko za ta buga wasanta na daf da kusa da na karshe na quater final da Kamaru da ta lashe kofin AFCON sau biyar, wacce ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-1 a daya daga cikin wasanni da suke fi daukar hankali, saboda Indomitable Lions ba ta taba doke Bafana-Bafana a wasanni biyar da suka taba gudanarwa a baya ba. A hakikanin gasakiya ma dai, 'yan Afirka ta Kudu suka mamaye wasan a fannin samun kyawawan damarmaki, yayin da 'yan Kamaru suka yi amfani da hazaka da basirarsu wajen ganin bayan Afirka ta Kudu, da ta taba lashe kofin a 1996, kuma ta kai matakin  kusa da na karshe a  a gasar da ta gudana a Côte d' Ivoire.

Sai dai nasarar da Lions indomptables ta samu ya zo wa 'yan Kamaru a ba zata saboda tawagar ta fuskanci tarin rikice-rikice kafin a sabunta wa'adin shugabancin FECAFOOT a karkashin Samuel Eto'o Fils da nada dan asalin kasar David Pagou a matsayin sabon mai horaswa, kamar yadda za ku ji cikin wannan rahoton da Zakari Sadou ya aiko mana daga Douala.

A ranar Asabar kuwa, Mali ta yi nasarar kawar da Tunisiya daga kasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida duk da raunin da kungiyar ta samu bayan da aka yi wajen road da dan wasanta Wolo Coulibaly a minti na 26 bayan da ya yi wa Hannibal Mejbri keta. Daga nan 'yan Tunisiya suka yi ta saba kwallo suna juya ta har lokacin da Firas Chaouat ya zuwa kwallo a minti na 88.

Mali da TunisiyaHoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto/picture alliance

Amma 'yan Mali sun farfado tare da kara kaimi a mintunan da aka kara bayan cikan mintuna 90, lamarin da ya sa su cin gajiya fenariti inda Lassine Sinayoko ya farke kwallon da ake binsu. Daga bisani kuma, Mali ta yi raba ni da yara a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya biyo baya.

Ita dai Kungiyar Aigles du Mali za ta kara da Lions de la Teranga ta Senegal a zagaye na uku na quater final, bayan da cikin sauki da araha Senegal ta kawar da Sudan da ci 3-1. Godiya ta tabbata ga Pape Gueye da ya zura kwallaye biyu a rabin farko, yayin da Ibrahim Mbaye ya zura kwallo na uku a ragar Sudan. Alhali Sudan ce ta fara wasan da kafar dama, inda Abdallah ya zura kwallon farko a minti na shida a wani hari da dakarun baya na Senegal suka kasa tsarewa.

A wannan Litinin ne ake ci gaba da wasanni zagaye na biyu, inda Masar da ta lashe kofin kwallon kafa na kasashen Afirka sau bakwai ke fafatawa da Benin, yayin da  Mozambique ke buga wasanta da Super Eagles ta Najeriya wacce ta taba lashe AFCON sau uku, inda na 2013 ya kasance na karshe. Sannan a gobe Talata, Aljeriya za ta fafata da DR Kwango, yayin da Côte d' Ivoire za ta kara da Burkina Faso.

A nan Turai kuwa, ba a gudanar da wasannin babban lig na kwallon kafar Jamus na Bundesliga ba sakamakon hutun shiga sabuwar shekara. Amma dai sauran manyan lig na wannan nahiya sun dora inda suka tsaya.

A Italiya, Inter Milan ta sake komawa matsayi na farko a gasar Italiya bayan da ta baje Bologna da ci 3-1, amma har yanzu tana fuskantar barazana daga AC Milan da Napoli, wadanda suka lashe wasansu na mako na 18. Amma sakamakon wannan nasara ta biyar a jere a gasar, Inter tana da maki 39, inda ta yi wa abokiya hamayyarta AC Milan zarar maki daya, yayin da ta fi Napoli da maki biyu. A kasan teburin Serie A kuwa, Fiorentina ta bar matsayi na karshe a hannun Pisa saboda nasarar da ta samu a karo na biyu a kakar wasa da ci 1-0.

Hoto: Dave Winter/FEP/Icon Sport/Sipa USA/picture alliance

A Faransa kuwa, Paris Saint-Germain ta fara shekarar da kafar dama inda ta doke takwarta Paris FC da ci 2-1 a mako na 17 na Ligue 1. Wannan wasan derby na farko a cikin shekaru 35 tsakanin kungiyoyin biyu na babban birnin Faransa, ya sanya PSG a matsayi na biyu da maki 39. A nata bangaren,

Marseille ta fara shekarar 2026 a cikin mummunan yanayi na rashin nasara 0-2 a hannu Nantes, lamarin da ya jefa ta a matsayi na uku da maki 32, yayin da Lens ke saman teburi da maki 40. Ita kuwa Metz  da take sahun 'yan baya ga dangi, ta yi takaicin ganin Lorient ta rama kwallon da take binta (1-1) bayan ta jagoranci wasan a mafi yawan lokuta.

A Ingila, Manchester City da Liverpool sun bar nasara ta salube musu a cikin 'yan dakikaon karshe a ranar Lahadi, a fafata da suka yi da Chelsea (1-1) da Fulham (2-2), wanda hakan ya kawo tsaiko ga burinsu a Premier League, a daidai lokacin da Arsenal ta daura damarar lashe gasar a bana. Manyan kungiyoyin da suka yi nasara a wasan mako na 20 na Ingila su ne Arsenal da ke saman teburi da maki 48, da Aston Villa da ke a matsayi na uku da maki 42. Ita kuwa Liverpool da ke rike da kambun zakara tana a matsayi na hudu da maki 34 bayan da ta yi kunnen doki da Leeds  0-0 . Ita ma Manchester United ta yi kunnen doki a wasanni biyu a jere.

Idan muka koma Spain kuwa, sakamakon barazana da Real Sociedad ta yi mata, Atletico Madrid ta yi kunnen doki 1-1 a ranar Lahadi a wasan mako na 18 na gasar La Liga, wanda hakan ya sa ta rasa maki masu mahimmanci a gasar. A yanzu dai Atlético mai matsayi na hudu da maki 38 ta sake samun kanta a bayan abokan hamayyarta biyu, musamman ma FC Barcelona da ke saman teburi da maki 49 da Real Madrid da ke matsayi na biyu da maki 45, yayin da Villarreal ke a matsayi na uku da maki 38 tare da kwantai na wasanni biyu.

Fitaccen dan wasan Tennis Novak Djokovic iHoto: Corinne Dubreuil/ABACAPRESS/IMAGO

A fegen tennis, Novak Djokovic dan kasar Sabiya ya sanar cewa zai bar kungiyar 'yan wasa PTPA da aka kafa tare shi a shekarar 2020, yana mai ambato "damuwarsa game da shugabanci" na wannan kungiya da ta balle daga hadakar 'yan wasan tennis ta duniya. Tun a watan Maris na 2025 ne dai, lamba 4 na duniya da dan kasar Kanada Vasek Pospisil suka shigar da karar shugabannin kungiyar kwararrun 'yan wasan Tennis (PTPA), inda suka yi Allah wadai da tsarin shirya jadawalin wasanni, inda ake wasanni a watanni 11 daga cikin 12 da ake da su a shekara.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Novak Djokovic mai shekaru 38, wanda ya lashe gasar Grand Slam sau 24 ya ce: Ina alfahari da hangen nesa da shi da Vasek suka yi wajen kafa PTPA domin ba wa 'yan wasa dama mai karfi da 'yanci, amma kuma dabi'unsa da muradansa ba su dace da alkiblar da kungiyar ta dosa a halin yanzu ba. Saboda haka ne fitaccen dan wasan na tennis ya yanke shawarar  mai da hankali kan wasansa tennis da, iyalinsa, da kuma ba da gudummawar ga wasanni da ke mutunta ka'idodinsa da kare mutuncina.

Djokovic, zai shiga gasar ATP 250 a Adelaide daga 12 zuwa 17 ga watan Janairu, don shirya shiga gasar Australian Open daga 18 ga watan Janairu zuwa daya ga watan Fabrairu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani