1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta hana magana kan rashin lafiyar Paul Biya

Zakari Sadou
October 11, 2024

Gwamnatin Kamaru ta haramta wa kafafen yada labaran kasar yin magana kan rashin lafiyar shugaba Paul Biya a daidai lokacin da ake rade-radin cewa shugaban mai shekaru 91 na fama da matsananciyar rashin lafiya,

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Cikin wata wasika da ya aike wa gwamnonin jihohin kasar goma, ministan  cikin gida Paul Atanga Nji, ya ce tattaunawa kan rashin lafiyar shugaban babban laifi ne da ya shafi tsaron kasa don haka gwamnoni su dauki matakin da ya dace don hukunta wadanda suka saba wannan umarni. Dan jarida kuma tsohon mamba a hukumar kula da kafofin yada labarai a Kamaru Christophe Bobiokono ya ce Paul Atanga Nji ya wuce gona da iri cikin ayyukansa. Sanarwar ministan ya ta da hankalin kungiyoyin farar hula da dama da suka ce wannan na nuna yadda ake hana yan jarida fadin albarkacin baki a kasar.

Hoto: picture alliance/abaca/E. Blondet

''Wannan minista bai da wannan hurumi, babu wata doka da ta bashi damar magana akan aikin yan jarida, hukumar kula da kafofin yada labarai ce ke da wannan hurumin, ministan harkokin cikin gida ba zai iya yanke hukunci akan labarun da ake yadawa ba''

Daraktan jaridar Horizon Nouveaux a Douala Nkodo Pierre Claver gwamnati da hukuma da ke kula da kafofin yada labarai na kokarin sanya matakai don yaki da fadawa rikicin siyasa da zai iya tunzura kasar cikin mummunar hali bayan shekaru 64 da samun yancin kai. Wannan dambarwa na zuwa ne yayin da zaben shugaban kasa na 2025 duk ke gabatowa da kuma rashin tabbas kan yan takara da za su fafata a zaben.

Hoto: Reuters/Z. Bensemra

A cewar wani rahoton kungiyar kare hakkin yan jaridu ta Duniya, Reporters sans frontieres Kamaru ce ke sahun gaba cikin kasashen da aka fi musgunawa yan jarida cikin ayyukan su a yankin Afirka ta tsakiya.

An yi wa Biya ganin kaarshe ne a taron kasashen Afirka da China da aka yi a birnin Beijing a watan Satumba. Bai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a birnin New York ba, ko kuma taron kasashe masu magana da harshen Faransanci a birnin Paris. Biya, wanda shi ne shugaban da ya fi tsufa a duniya, an daina jin duriyar sa tun a farkon watan Satumba, lamarin da ya karfafa jita-jitar da ake yadawa a yanar gizo cewa rashin lafiyar ya tabarbare. Fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa Biya na cikin koshin lafiya.