1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta karyata jita-jita a kan Shugaba Biya

October 9, 2024

Gwamnati a Kamaru ta ce babu gaskiya cikin labaran da ke yawon cikin jama'a game da halin da shugaban kasar yake ciki, bayan kwashe lokaci ba tare da an ga Shugaba Paul Biya ba.

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru
Shugaba Paul Biya na kasar KamaruHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru, sun kore rade-raden da ake yi dangane da halin lafiyar Shugaba Paul Biya mai shekaru 91, bayan kwashe lokaci ba tare da ya fito a bainal jama'a ba.

Jami'ai a Kamarun sun ce Shugaba Biya na cikin halin lafiya, kuma yanzu haka yana ziyara ne a nahiyar Turai.

Cikin watan jiya ne dai aka ga shugaban na Kamaru a cikin jama'a, a lokacin taron da China ta yi da shugabannin kasashen Afirka a birnin Beijing.

Sai dai tun daga wannan lokacin ba a sake ganin sa ba; hatta a lokacin babban taron majalisar Dinkin Duniya da shugabannin kasashe suka halarta a Birnin New York.

Haka ma a lokacin taron koli na shugabannin kasashen da ke amfani da harshen Faransanci da aka yi a kasar Faransa.

Galibi Shugaba Paul Biya kan ziyarci nahiyar Turai musamman domin duba lafiyarsa.