SiyasaAfirka
Jami'an tsaro sun hana zanga-zangar Kamaru
September 22, 2020Talla
Jama'a dai ta yi jerin gwano a titunan Douala, inda wasu suka rike tutar Kamaru, suna fadin kalamai munana kan gwamnatin Shugaba Paul Biya.
Tun da farko madugun adawar kasar Maurice Kamto ya kira zanga-zangar domin matsawa gwamnati lamba ta tsagaita wuta a rikicin 'yan awaren kasar da kuma kawo sauye-sayue a hukumar zaben kasar.
To sai dai kuma masu zanga-zangar sun sha da kyar bayan da jami'an tsaro suka watsa musu hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su. Kazalika akwai wasu wadanda suka shiga hannun jami'an tsaron a matsayin masu kunnen kashi.