1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Take hakkin jama'a na ci gaba da muni a Kamaru

December 10, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta ware rana ta musamman saboda kare hakkin bil Adama, sai dai ga alama ba haka lamarin yake a Kamaru ba ganin yadda hukumomi ke tsare mutane ba bisa ka'ida ba.

Kamerun l Gefängnis in Kondengui, Sicherheitskräfte Polizei
'Yan sanda a harabar gidan yarin Yaounde na KamaruHoto: cc by M. E. Kindzeka (VOA)

Daya daga cikin misalin wadanda hukumomin Kamarun suka tsare ba bisa ka’ida ba, shi ne wani haifaffen kasar Jamus da iyayensa ke da tushe da kasar, Wilfried Siewe, wanda aka kama cikin watan Fabrairun bara. Wilfried Siewe wanda aka saka a makon jiya, da a yanzu ke tare da iyalinsa a nan Jamus, ya yi zaman daurin ne a gidan yarin birnin Yaounde na kusan shekaru biyu.

Karin Bayani: Ana zargi gwamnati Kamaru da take hakkin fursunoni

A hirar da ta yi da tashar DW, mai dakin Mr. Siewe, ta bayyana yadda ta ji da dawowar mijin nata da kuma fatan ganin yadda zai koma rayuwarsa yadda ya saba, ya ce ya yi matukar farin cikin sake gamuwa da iyalinsa, yana mai cewa "Mawuyacin yanayi ne kwarai da ni kaina ba zan iya cewa ga yadda za a iya kai karshensa ba." Yanzu abin da ya fi so shi ne yadda zai dawo da harkokinsa yadda ya saba a baya. Ina son mika godiyarmu ga dukkanin wadanda suka taimaka wajen ganin an sako shin. Wifred Siewe bai sami damar magana ba ne saboda a halin yanzu yana killace saboda corona. 

Zanga-zangar kin jinin gwamnatin Kamaru

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati Hoto: DW/H. Fotso

Hukumomin kasar Kamaru sun kama shi ne saboda zarginsa da shiga zanga-zangar adawa da Shugaba Paul Biya da aka yi a birnin Berlin, zargin kuma da ya musanta. Yayin da shi Wifred Siewie ya samo kansa daga kurkuku, a share guda kuwa dubban ‘yan kasar Kamarun ne ke ci gaba da zama a garkame. Mancho Bibixy, wani dan jarida ne kuma mai fafutuka da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 16 saboda zanga-zangar lumana da ya yi a Kamaru, kuma DW, ta yi magana da shi daga wajen da yake tsare, inda ya ce "Rayuwa ta yi mini matukar tsauri, kamar yadda take ga kowane mutumin da ke tsare. Musamman asancewar inda ake tsare da ni na da nisa da wajen da iyalina suke.  Abu na biyu kuma yanayin da ake ciki a nan da ya hada da cunkoso da karancin ruwa da wuta ga kuma yawan rashin lafiya da sauransu, duk su ne suka hadu suke maida rayuwa abin kaico." 

Karin Bayani: Gwamanti ta samar da zaman lafiya a Kamaru

Taka hakkin dan Adam ya munana a Kamaru

Gidan yarin Bamenda a KamaruHoto: picture-alliance/imageBROKER/R. Marscha

Ita ma a hirarta da DW, jagorar kungiyar kare hakkin jama’a a kasashen tsakiyar Afirka, Maximilienne Ngo Mbe wadda ke a birnin Doula, ta ce tsare Wilfred Siewe da Bibixy Mancho, dan takadirin misali ne na yadda lamarin ya tsananta a Kamaru. Ta ce batun Bibixy Mancho da Wilfried Siewe, tamkar babu abin ma da aka fada. Kama Mancho da aka yi wani babban misali ne na taka hakkin bil Adama a Kamaru. Hakan kuma tabbaci ne na yanda ake ta tsare masu rajin kare hakkin jama’a da wasu masu son zuciya ke ci gaba da yi.

Karin Bayani: Kacici-kacici 2020: Ranar ‘Yancin Dan Adam 2020

Ita kanta Maximilienne Ngo Mbe, ta sha fuskantar cin mutunci da ma hare-hare a Kamarun, abin da kamar yadda take fadi tabbaci ne kan yadda gwamnatin Shugaba Paul Biya ke tafiyar da tsarinta na dimukuradiyya, tana bayyana munin halin da masu kare hakkin bil Adama ke a ciki a kasar, tamkar matsayin rai da mutuwa. Haka ma akwai zargin gwamnatin ta Kamaru, na ci gaba da tsare dubban mutanen da suka fito daga yankin kasar na renon Ingila.