1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Rashin tsaro da batun ilimi a Kamaru

Zakari Sadou LMJ
September 5, 2023

A daidai lokacin da ake koma wa sabon zangon karatu na shekara ta 2023 zuwa 2024 a Kamaru, yara da dama ba su koma makarantunsu ba a yankin da ke magana da Turancin Ingilishi sakamakon fargabar rashin tsaro.

Kamaru | Kumba | Hari | Makaranta
Hare-haren 'yan bindiga, ya tilasta yara da dama daina zuwa makaranta a KamaruHoto: Tamfu Ciduan Ndimbie/My Media Prime TV/Reuters

An dai tsammaci yara miliyan takwas ne za su koma bakin karatu a zangon karatun na bana a Kamarun, sai dai a zahiri ba haka wannan kiyasin ya kasance ba a yankunan masu amfani da Turancin Inglishi. Bayan watanni hudu na hutu ne 'yan makarantar firamare da sakandire suka koma sabon zangon karatu na shekarar ta 2023 zuwa 2024 a Kamaru, a cikin yanayi na rashin tabbas a yankunan da ke fama da rikicin 'yan aware a Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yammacin kasar. Yayin da 'yan tawaye suka yi harbin kan mai uwa da wabi domin hana yara da malamansu koma wa makarantun a yankin, an halaka wata daliba mai shekaru 16 a Kumba da ke Lardin Meme da kuma malaman makaranta uku. Wani malamin makarantar firamaren gwamnati da ke garin Kumba da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce, ya yi kokarin zuwa kasuwanni da masarautu domin shawo kan iyayen yara su bar yaransu su koma makaranta amma bai samu hadin kansu ba.

Hari kan yara 'yan makaranta a Kamaru

03:28

This browser does not support the video element.

Wasu iyayen yaran sun yi adawa da kiran da gwamnatin Yaounde ta yi musu da su bar yaransu su koma makarantun, saboda babu tabbacin ingantaccen tsaro da zai kare yaransu daga hare-haren 'yan bindiga. Kimanin makarantu sama da dubu uku da 285 ne suke rufe sakamakon hare-hare ko barazanar 'yan bindiga musamma ma a yankunan na masu magana da Turancin Inglishi, kuma sama da yara dubu 800 sun kaurace wa makarantu kamar yadda hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cikin wani rahotonta da ta fitar a shekarar 2021 zuwa 2022. Kawo yanzu a Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru, makarantu da dama sun kasance a rufe sakamakon barazanar kai hari. An dai kafa dokar hana fita da ta samu karbuwa daga al'ummar yankin, haka ma abin yake a mafi yawan kauyukan Arewa maso Yammacin kasar da ke zaman tushen rikicin da gwamnatin  ta kasa magance shi.