Rikici gabanin babban zabe a Kamaru
October 1, 2018Wannan lamari dai na zuwa ne kasa da mako guda a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kamaru, lamarin da ya saka gwamnatin kasar kafa dokar hana fita da zirga-zirga da duk wasu tarukan jama'a a yawancin biranen yankin masu magana da harshen Turancin Ingilishin na Anglophone. Yunkurin da ya kasance mataki na neman hana wa 'yan awaren tayar da tarzoma.
Yanzu haka dai al'umar yankin na masu magana da harshen Turancin Ingilishin a kasar ta Kamaru na cikin zaman fargaba ta la'akari da asarar rayukan da aka samu a shekarar bara, lokacin dauki ba dadin da ya biyo bayan ayyana 'yancin kan yankin na Ambazoniya, inda 'yan sanda suka bindige masu zanga-zanga akalla arba'in. Wannan kasa da ke yankin tsakiyar Afirka mai mutane kimanin miliyan 25, ba ta taba fuskantar zabe a yanayi na tabarbarewar tsaro da ya yi muni kamar wannan karon ba, dalilin da ya sanya aka jibge jami'an tsaro a yankuna uku daga cikin goma na kasar.