Kame babban Akanta na Najeriya, babu tabbas?
May 17, 2022Komar hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriyar ta yi babban kamun wanda aka dade ba a ga irin sa ba, domin kame babban jami'in da ke kan ganiyarsa ta aiki da ta yi babban al'amari ne. A sanarwar da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce tana zargin Ahmed Idris Akanta Janar na kasar ne da binciken kwakwaf da ta gudanar ya gano yadda ya yi amfani da kamfanoni na ‘yan uwa da abokan arziki. Ana zargin sa da sayen manyan gidaje na alfarma a Abuja da ma a birnin Kano.
Masu cin hanci da rashawa dai sun dade suna barna a Najeriyar inda suke gurgurar tattalin arzikin kasar tamkar yadda gara ke yi wa katako in ta same shi. Akanta Janar din na Najeriya ya dade yana fuskantar bincike da ta kaiga aika masa da gayyata amma kuma ya yi biris da ita.
Duk da girman laifin da ake zargin sa da aikatawa ya kaiga cafke shi da jami'an hukumar ta EFCC suka yi, inda Akanta Janar din yake can yana amsa tambayoyi, Malam Bashir Baba masanin al'amurran yau da kullum ya ce akwai abin da yake tsoro da daukacin lamarin.
Cin hanci da rashawa dai ya zama daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Najeriya, inda masu cin hancin suka hana kasar sakat na tsawon shekaru, abin da Major Hamza Al Mustapha ya bayyana da mutane 54 suka hana kasar sakat.
A 2015 ne dai shugaban Najeriya ya nada Ahmed Idrsi a matsayin babban Akanta na kasa kuma duk da cikar wa'adinsa na yin ritaya na shekaru 60 sai aka kara masa wani sabon wa'adin a 2019 kafin wannan al'amari ya afku da shi.
Za a sa ido a ga yadda za ta kaya bayan kame shi da hukumar ta yi bisa wannan zargi na kudadde masu yawan gaske a kasar da ke hakikancewa a kan tana yaki da masu halin bera da suka hana kowa sakat.