Kame baki a Kano
June 22, 2013Sakamakon rikice-rikice da suka yi tsamari a Arewacin Tarrayar Najeriya, hukumar kula da shige da fice ta kasa ta fara farautar bakin dake shigowa yankin arewacin kasar da nufin tantance wadanda ke zaune ba bisa ka'ida ba. Koda yake ba wannan ne farau da ake kame bakin a Najeriyar ba, amma dai sabon kamen na zaman mafi girma da aka tattara daruruwan bakin, aka kuma tura su zuwa kan iyakokin kasashen su. Daruruwan 'yan Nijar da Chadi da kuma Mali ne aka kamo, aka kuma tattara a harabar hukumar shige da fice ta kasa dake birnin Kano.
Wannan dai ya biyo bayan dokar ta-baci da aka san'ya a jihohi uku na yankin arewacin Najeriyar, abinda a yanzu hukumomin ke zargin ya sa ana samun kwararar bakin hauren zuwa wasu jihohin na arewa.
Dama dai hukumomin Nijeriya sun dade suna zargin bakin haure da makwabtan kasashen wajen da hannu a rikice rikice dake addabar arewacin kasar.
Hamisu Muhammed Mai Shanu, shine babban jami'in hukumar shige da fice a jahar Kano, yace matakin ya faru ne domin gwamnatin Najeriya na bukatar ganin duk wani bako yana zaune bisa ka'ida a kasar. Galibin wadanda aka kama dai sun fito ne daga jamhuriyar Nijar sai kuma kasar Chadi da Mali. Abdulaziz matashi ne da aka kama ake kuma shirin mayar da shi gida jamhuriyar Nijar, yace shi dai babban burinsu shine samun fita lafiya daga hannun jami'an hukumar. Shi kuma Muhammed Saleh, matashi ne wanda yace haifaffen Najeriya ne, amma kuma iyayensa 'yan asalin kasar Chadi ne, yace bai ga dalilin kamun da aka yi masa ba.
Hukumar ta shige da fice a jihar Kano, ta bakin shugaban ta Muhmmed Hamisu Mai Shanu, tace wannan kamu na bakin yana da alaka da dokar ta-baci da aka san'ya a jihohin Borno da Yobe da kuma jahar Adamawa,
Koda yake dai bamu yi katarin samun wakiliyar jamhuriyar Nijar a jihar Kano ba, amma dai wasu jami'ai a ofishinta sun ce dama an dade ana yin wannan kame, amma wannan ne dai gagarumi. Sai dai ofishin yana kokarin tattaunawa da mahukunta domin kamo bakin zaren matsalar.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Usman Shehu Usman