Kame-kamen 'yan adawa a Masar
November 28, 2014Talla
Ofisfin ministan tsaron cikin gidan kasar ta Masar ne ya sanar da kame mutane akalla 107, kafin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da suka shirya gudanarwa a wannan Jumma'a. Tun dai kifar da gwamnatin Mohamed Morsi, sabbin hukumomin kasar ta Masar ke shan gwagwarmaya tare da neman toshe duk wata kafa ta zanga-zanga ga magoya bayan tsofon shugaban kasar, inda ake zargin su da shirya zanga-zanga mai muni gami da tashe-tashen hankula.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Awal