1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
IlimiAfirka

Kameru da fasahar AI a makarantu

September 29, 2026

Hukumomin Kamaru sun fara shigar da fasahar kirkira ta AI cikin tsarin karatu daga wannan shekarar. Sai dai wannan na zama wani sabon kalubale ga iyaye na kashe kudi a kan intanet a yanayi na matsin tattalin arziki.

Fasahar AI
Fasahar AIHoto: Li Ying/Xinhua/dpa/picture alliance

A Kamaru, hukumomin ilimi sun fara shigar da fasahar kirkira ta AI cikin tsarin karatu daga wannan shekarar. Sai dai wannan na zama wani sabon kalubale ga iyaye na kashe kudi a kan intanet ga daliban a cikin yanayi na matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

Marcelle, mai shekaru 14, ɗaliba ce da ke ajin troisième na sakandare, hankalinta na kan wayar mahaifiyarta. Tana fuskantar wata jarabawar lissafi mai wahala, kuma darasin da ta dauko daga makaranta ba su wadace ta ba. Saboda haka sai ta nemi taimakon manhajar kirkirarriyar basira.

Kudin da ake bukata

Amfani da Fasahar AI a makarantuHoto: DW

Kudin rajistar makaranta da na kungiyar iyaye da malamai sun kai kusan CFA 32,500. An riga an tsara kudin sayen littattafai. Amma yanzu wata hanyar sabuwar kashe kudi ta bayyana daga bangaren fasahar zamani.

Wannan sabuwar hanyar kashe kudi na kara fadada gibin da ke tsakanin masu hali da marasa shi wajen samun damar amfana da fasahar zamani. Siyen intanet mara iyaka a gida ga manyan ma'aikata ya zama wani abin da suka fi bai wa fifiko, yayin da marasa karfi ke shan wahala sosai domin samar da ita.

Manhajar tallafa wa dalibai a Habasha

03:12

This browser does not support the video element.

Daga yanzu dai daliban makarantun sakandare na iya amfani da fasahar a yayin jarabawa domin samun karin bayanai da zurfafa bincikensu a kasar ta Kamaru.

Sai dai a yayin da ake jiran yiwuwar samar da wani tsari na musamman da za a yi amfani da shi, iyaye da dama na ci gaba da 'yan dabaru da kudadensu, suna fama da kashe kudin sayen intanet wanda yanzu ya zama mafi tsadar abin da ake kashewa wajen karatun yara.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW