Kamfanin Boeing zai sallami ma'aikata 17,000
October 12, 2024Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya sanar da cewa zai rage kashi 10 cikin 100 na ma'aikatansa a fadin duniya a cikin watanni masu zuwa, lamarin da ka iya shafar guraben aiki akalla 17,000. Kamfanin mallakin Amurka ya kuma ce yana duba tsaren-tsarensa na kera jirage a kokarin da yake na shawo kan matsalolin kudade da yake fuskanta.
Karin bayani: An hana Boeing 737 MAX shiga wasu kasashen
A cikin wasu sakonni guda biyu da ya aike, kamfanin kera jiragen saman ya ba da sanarwar cewa za a samu karin jinkiri wajen kammala kera sabon sunfurin jirginsa mafi girma 777X da kuma daina kera jirage sunfurin 767 a shekarar 2027.
Kamfanin Boeing dai ya fada cikin tsaka mai wuya ne sakamakon kura-kurai da aka samu a jiragen da ya kera a baya-bayan nan, musamman ma hadarin da wani jirgi kirarsa na kamfani Alaska Airlines ya yi a farkon watan Janairu na wannan shekara.