1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kamfanin jiragen sama na Lufthansa zai rage ma'aikata 4,000

September 29, 2025

Kamfanin Lufthansa ya ce zai rage ma'aikata 4,000 daga nan zuwa shekara ta 2030, sakamakon karancin samun kudin shiga.

Jiragen kamfanin Lufthansa
Jiragen kamfanin LufthansaHoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/picture alliance

kamfanin na Lufthansa ya fuskanci cikas dangane da yadda yake gudanar da al'amuransa idan aka kwatanta da sauran takwarorinsa da ke sauran kasashen nahiyar Turai, inda kamfanin ya koma mataki na biyar a 2024.

Karin bayani:Yajin aiki ya tilasta rufe filin jirgin saman Frankfurt na Jamus 

Kamfanin da ke kula da harkokin zirga-zirgar jiragen saman Eurowings da Austrian da Swiss kuma Brussels Airlines ya yi hasashen samun ribar euro miliyan 300 daga 2028 zuwa 2030. Baya ga kamfanonin jiragen sama a Jamus da ke fuskantar kalubale, akwai kamfanoni da dama ciki har da na sufurin motoci da suka sanar da rage yawan ma'aikata.

Karin bayani:Lufthansa: Ma'aikatan cikin jirgi za su tsunduma yajin aiki 

Kungiyar kwadago ta Verdi da ke wakiltar ma'aikatan kamfanin na Lufthansa ta sha alwashin yin fatali da duk wani yunkuri na rage ma'aikata.