1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamfanin NNPC a Najeriya ya yi shelar neman abokan hulda

October 30, 2025

Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriya NNPC ya mika kokon bararsa ga kwararru da zasu yi amfani da fasaharsu wajen farfado da matatun mai guda uku da ke neman durkushewa a kasar.

Matatar mai na Kaduna a Najeriya
Matatar mai na Kaduna a NajeriyaHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Shugaban kamfanin Bayo Ojulari shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce idan aka farfado da matatun man da kuma aikin da Dangote yake yi na fitar da ganga dubu 445,000 a kowacce rana zai taimaka wajen bunkasa samar da mai a kasar da kuma dagaro da Najeriya ke yi wajen fitar da gurbataccen mai kasashen ketare domin sarrafawa.

Karin bayani:NNPC: Matatar mai ta Fatakwal za ta koma aiki

A baya dai tsohon shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya rattaba hannu kan kwangilar dala biliyan $2.5 domin farfado da matatun man guda uku, to amma har yanzu ba a kai ga aiwatar da shirin ba.