1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamfanin tsaron Amurka zai shiga Afirka ta Tsakiya

December 27, 2023

Wani kamfanin tsaro na kasar Amurka na shirin fara harkoki a Afirka ta Tsakiya. Gwamnati dai ta tabbatar da wannan batu da ake yi wa fassara iri dabam-dabam.

Wani sojan ketare a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta Tsakiya
Wani sojan ketare cikin jama'a a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta TsakiyaHoto: Leger Kokpakpa/REUTERS

Kamfanin tsaro mai zaman kansa na kasar Amurka mai suna Bancroft Global Development, ya ce yana kan tattaunawa da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a kan wasu ayyuka da za su yi tare a nan gaba, wani abu da ake fassara shi da yiwuwar tsame hannun kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner, a kasar da ke fama da rikice-rikice.

Kamfanin wanda ya kore batun jibge jami'ansa ko kuma fara aiki a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, a gefe guda ya amince cewa tattaunawa ta yi nisa a tsakaninsa da gwamnatin Shugaba Faustin Touadera.

A farkon watan Yulin da ya gabata ne kamfanin na tsaro na Amurka wato Bancroft, ya amince da tattaunawa a kan ayyuka da zai yi a nan gaba a game da tsaro a kasar.

Cikin makon jiya ma dai kakakin fadar shugaban Afirka ta tsakiya Albert Yaloke , ya fada ta kafar watsa labaran cikin gida cewa kasar na kokarin fadada hanyoyin inganta tsaronta da wasu kasashen duniya.