Kamfanonin Jamus a Afirka
March 27, 2013Nahiyar Afirka dai nahiya ce da Allah ya huwace mata tarin albarkatun karkashin kasa irinsu man fetur da gas da ja da farin karfe da ke zaman tamkar mafarki ga sauran nahiyoyi. Dalilin kenan da ya sa sauran kasashen duniya ke sha'awar shiga wannan nahiya tamu domin yin cinikin ba ni gishiri in ba ka manda wato suke musayar ayyukan fasaha da danyun albarkatu. A dai halin yanzu kamfanonnin kasar Jamus na neman damar shiga wannan nahiya inda tuni kamfanonnin China suka dade da baje kolinsu.
Tuni kamfanin Herrenknecht ya shiga Afirka
"Duk wanda ya yi alaka da mu a aikin tone kasa to zai samu huldodi": Taken kenan na kamfanin Herrenkenecht AG da ke garin Schwanau na yankin Schwarzwald da ke Jamus wanda ke mallakar manya-manyan injinunan da ake amfani da su wajen gina hanyoyin karkashin kasa. Kamfanin Herrenknecht yana gudanar da aikin gine-gine a sassa dabam-dabam na duninya,, kama daga birnin Abu Dabi da St. Petersberg na Rasha zuwa kasar China da birnin Berlin na Jamus zuwa birnin Istanbul na Turkiyya da kasar Afirka ta Kudu. Ulrich Schaffhauser da ke kula da sashin kamfanin da ke gina hanyoyin karkashin kasa ya yi karin bayani:
"Akwai manyan-manyan ayyuka da muke gudanarwa a Afirka ta Kudu da suka hada da gina layin dogo da hanyoyin karkashin kasa. Akwai wasu kananan ayyuka da muke yi a fannin gina magudanar ruwa. To sai dai abin da muke samu a wannan kasa bai taka kara ya karya ba kasancewar kwangiloli kadan ne muke samu a can. Ba zamu dade muna aiki a wannan kasa ba."
Kanfanin Herrenknecht na kuma aiki a kasashen arewacin Afirka da suka hada da Aljeriya da Maroko da Masar. A dai halin yanzu kamfanin ba shi da manufar shiga yankin tsakiyar Afirka har sai an samu lafawar kura a wannan wuri. Anan ma Schaffhauser ya yi karin bayani da cewa::
"Abin kuma da ke da muhimmacin shi ne halin tsaro da ya kamata mu kalla da idon basira. Bayan mun samu tabbacin tsaro mu kan dubi yawan jama'a a duk sanda za mu yi aikin gina magudanar ruwa. Hakazalika muna mai da hankali ga kudin da aikin zai kunsa. Hakan kuwa na da nasaba ne da danyun albarkatun da kasar ke da su. Idan kuwa har ya zamana kasar na da wadannan albarkatu to za ta samu kudaden gudanar da wannan aiki a saukake. Muna kuma dubawa mu gani ko da wani rance da kasar ke samu daga bankin duniya ko kuma da wani tallafi da take samu daga masu zuba jari daga ketare".
Kamfanonin Jamus na shirin shiga Najeriya
A dai halin yanzu kamfanin Herrenknecht na hangen hanyar shiga Najeriya. Kuma a baya ga kasuwar da ke akwai a Afirka ta kudu a halin yanzu akwai jerin kasashen Afirka da kamfanonin Jamus ke son yin aiki tare da su. A nahiyar Afirkan ne ma ake samun kashi 21 daga cikin dari na kamfanonin Jamus da ke aiki a ketare. To sai dai sakamakon wani bincike da kungiyar aikin masana'antu da ciniki ta Jamus ta gudanar ya bayyanar da cewa a cikin shekara guda da ta gabata an samu kashi 18 daga cikin dari na kamfanonin Jamus da ke aiki a Afirka. Heiko Schwiderowski da ke kula da harkar kungiyar a Afirka ya ce yawan ayyukan fasaha da Jamus ke yi a Afirka ya zarta yawan hajojojin da take aikawa zuwa wannan nahiya.
"Yawancin kamfanonin sun fi mai da hankali ne akan ayyukan samar da ababan jin dadin rayuwa.Da dama daga cikinsu injiniyoyi ne. Akwai kuma kamfanonin da ke aiki a fannin ilimi da kayan aikin na ilimin kiwon lafiya suke kuma kai fasahohi dabam-dabam."
Idan dai aka kwatanta da sauran kasashen duniya Jamus na akan gaba wajen sayar da takalman yara a kasuwannin Afirka inda a wancan shekara ta sayar da takalman da kudinsu ya kama Euro miliyan dubu 21 daga cikin cinikin da ta yi na Euro miliyan dubu har sau dubu 1 da doriya a duniya.
Mawallafiya: Sabine Kinkartz/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal