1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

210809 Wasser Dürre Kenia

August 25, 2009

Samun ruwan sha mai tsabta sai wane da wane a wasu sassa na babban birnin ƙasar Kenya, musanman jama’a dake zaune a wata unguwar talakawa.

Fari a KenyaHoto: DW /Maya Dreyer

A wannan unguwa, mutane na fama da tsanannin ƙarancin ruwan sha da na amfanin yau da kullun, inda har matattarar ruwa da gwamnati ta tanadar don amfani a lokacin ƙarancin ruwa ta shanye.

A unguwar Kangemi farashin ruwa ya yi tashin gwauron zabbi. Wani saurayi mai sayar da ruwa Paul Paul Mwangi ya ƙara kuɗin bokiti ɗaya na ruwa.

"Sule uku na kuɗin Kenya kwatan kwacin Naira 26 sune kuɗin galon ɗaya na ruwa a wannan unguwa, amma kuma a wasu unguwannin ma, akan sayar da galan ɗaya har sule 20 kwatankwacin Naira 70. Da yawa daga cikin al'umar wannan unguwar albashin su bai zarce Sule 100 a wuni ɗaya ba wanda a misali zai kama Naira 150."

Shi ma Paul bai iya tabbatar da samun waɗannan kuɗaɗe masu yawa nan gaba akan farashin ruwa da yake saidawa ba sabili da gwamnati ce ke ƙayyade farashin ruwa a ƙasar Kenya.

"Idan na yi lissafi da farashin sauran kayan masarufi, da kuma kuɗaɗen sauran kayayyakin rayuwa da dole zan biya, sai inga kuɗin da nike samu na sayar da ruwa ba ya isata biyan bukatuna da na iyali."

Ruwan sha ya kasance wani abu mai matuƙar daraja ga al'umar ƙasar. Bayan bala'in fari da ƙasar ta yi fama da shi, matattarar ruwa da wasu tafkuna da jama'a ke samun ruwa yanzu haka duka sun kafe. Ganin haka ya sanya gwamnati ta ɗauki matakan ƙayyade adadin yawan ruwa da take bayarwa daga unguwa zuwa unguwa. Sau ɗaya ake sakin ruwa a kowace unguwa a cikin sati don fargabar ƙarewar ruwa gaba ɗaya.

Duk da mayuwacin hali da mazauna unguwar talakawa ke fuskanta na ƙarancin ruwa, hukumomi sai ƙara tsaurara matakai suke yi na samun rayuwa, haka kuma ‘yan kasuwa ke ƙara farashin kayan abinci.

David Soaer na ma'aikatar ruwa ya yi ƙarin bayani a game da sabbin tsare tsare na samun rowan sha.

"Daga nan ma'aikatar ruwa ne ake ƙayade yawan ruwa da za a sayar a ko wace rana, kuma mukan sayar da ruwa na kuɗin shilling 20 wato Naira 70 ga ko wani magidance. Idan mutum na bukatar sayen ruwa da adadinsa ya wuce na shilling 20 dole ne sai mu a ma'aikatar ruwa mun ba shi izini na musanman don yin haka."

Domin samun ruwa na biyan bukata a ko wace rana dole ne mazauna unguwar Kagemi su kusan wuni a ma'aikatar ruwa, amma kuma hakan ba zai yiwu ba domin wasu lalurorin yau da kulun inji Sylvia Ndikila ‘yar unguwar.

"Wajibi ne mu mazauna wannan unguwa mu cigaba da neman mafita. Yanzu haka ina da bukatar wanke kayana amma kuma galan ɗaya ko biyu kawai nake iya saye wanda ko girke girke da wanke wanken kwanuka tare da ruwan sha ne kawai, bayan kuma wahalar ɗaukan su zuwa gida."

Vivian ‘yar makaranta mai shekaru 14 da haifuwa tace suma ‘yan makaranta lamarin ɗaya ce.

"A makaranta wani lokaci sau ɗaya kawai muke cin abinci a rana sabili da rashin ruwa wani lokacin ma bama samun abinci har na tsawon wuni ɗaya. Batun abin sha kuwa, sai dai a manta."

Tuni aka daina wankin gidajen ba haya a makarantu dake unguwar Kangemi sabili da ƙarancin ruwa, duk da cewa fiye da mutane ɗari ke amfani da waɗannan muhinman wurare a kowace rana. Wani mazauni Kangami yace wuraren ba hayar dake unguwar duk sun cika amma kuma dole ne jama'a su nemo wata hanya.

"Da yawan mutane yanzu haka suna amfani da ledodi wajen yin ba haya daga baya su wurgar, don haka a duk inda ka shiga zaka ga waɗannan ledodi da ake yiwa suna Flying toilets suna yawo."

Masana sun yi kira ga gwamnatin Kenya da ta ɗauki matakan gaggawa don tinkarar matsalar ƙarancin ruwan. An kuma yi gargaɗi game da ire-iren matsalolin da wannan lamari zai iya janwowa ga lafiyar jama'a idan aka cigaba da haka nan gaba. Paul Mwangi mazauni Kangemi.

"Wajibi ne gwamnatin Ƙenya ta nemo mafita a game da matsalar ruwa a ƙasar. Idan ba haka ba abinda wani zai iya yi a game da matsalar ruwa. Kuma idan bata magance wannan matsala ba, to kuwa ta tabbatar da ta kasa biyan bukatun al'umarta."

Mawallafa: Antje Diekhans/Rabi Gwandu

Edita: Mohammad Nasiru Awal