1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

Zimbabuwe: Kammala babban zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2023

Al'ummar Zimbabuwe sun kada kuri'unsu a zaben da Shugaba Emmerson Mnangagwa ke neman tazarce, bayan da aka gudanar da yakin neman zabe cike da zargin kokarin murkushe 'yan adawa da karfin tuwo.

Zimbabuwe | Zabe | Emmerson Mnangagwa | Nelson Chamisa
Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Zimbabuwe mai cike da zarge-zargeHoto: Siphiwe Sibeko/Reuters

Mai shekaru 80 a duniya Shugaba Emmerson Mnangagwa da ke zaman dan jam'iyya mai mulki ta ZANU PF, ya dare kan karagar mulki bayan juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin shugaban kama-karya na mutu ka raba na kasar marigayi Robert Mugabe a 2017. A yanzu dai Mnangagwa na takara ne, tare da shugaban jam'iyyar adawa ta CCC Nelson Chamisa mai shekaru 45 a duniya.