1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala tseren keke a Kigali na Ruwanda

Mouhamadou Awal Balarabe SB
September 29, 2025

An yi kare jini biri jini a karawa da aka yi tsakanin Borussia Mönchengladbach da Eintracht Frankfurt a gasar Bundesliga inda aka yi ruwan kwallaye kana an kammala tseren keke na duniya da ya gudana a Kigali na Ruwanda.

Tseren keke a birnin Kigali na kasar Ruwanda
Tseren keke a birnin Kigali na kasar RuwandaHoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

A nan Jamus, an gudanar da wasannin mako na biyar na kakar wasannin 2025-2026 na Bundesliga, inda aka zura kwallaye 26  a wasanni tara da aka buga tsakanin kungiyoyi 18. Hasali ma dai, an zura kwallaye goma daga cikin su a filin wasa na Borussia Park a ranar Asabar, a yayin da Borussia Mönchengladbach ta karbi bakuncin Eintracht Frankfurt.

Duk da cewa Frankfurt ta yi nasara da ci 6-4, amma ta girgiza har karshen wasan, saboda ta gasa wa Gladbach aya hannu da ci 0-5 a lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci. kazalika dan wasan baya na Frankfurt Robin Koch ma ya zura kwallo bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Sai dai gada bisani Borussia Mönchengladbach ta farka daga magagin barci, inda ta zura kwallaye uku cikin mintuna 11, ko da yake sakamakon karshe ya nuna cewar ta makara, saboda Frankfurt ta bi Borussia Mönchengladbach har gida kuma ta fi ta iya taka rawa.

Lig na kasashen Turai

Wasannin Bundsliga na JamusHoto: Marcel Engelbrecht/firo Sportphoto/picture alliance

A game da sauran sakamakon wasannin kwallon kafa na Bundesliga kuwa, Bayern Munich ta mamaye Werder Bremen da ci 4-0, lamarin da ke ba ta damar ci gaba da jan zarenta a samen teburi bayan da ta samu nasara biyar a wasanni biyar. Ita kuwa Borussia Dortmund BVB na a matsayi na biyu da maki 13 bayan da ta bi Mainz har gida kuma ta doke ta da 2-0, ciki har da kwallon da Adeyemi da ke da tushe da Najeriya ya zura.

A nata bngaren, RB Leipzig, ta uku a saman teburi, ta yi nasara da ci 1-0 a Wolfsburg. Ita kuwa Bayer Leverkusen ta doke Saint Pauli da ci 2-1, yayin da Heidenheim ta doke Augsburg da ci 2-1. Amma Union Berlin da Hamburg sun tashi 0-0, yayin da Freiburg da Hoffenheim suka yi kunnen doki 1-1- A karshe kuma, Stuttgart ta biyo Köln har gida kuma ta lakaba mata duka ci 2-1.

A sauran manyan lig na kasashen Turai, AS Roma  ta fara tafiya kafada da kafada da AC Milan da Napoli a yawan maki 12 a gasar kwallon kafa ta Italiya bayan ta doke Verona da ci 2-0 a ranar Lahadi a wasan mako na biyar. Dama dai Milan da ke saman teburi a gasar Seria A ta samu nasara a kan Napoli da ci 2-1.

Wasannin La Liga na SpainHoto: Gongora/NurPhoto/picture alliance

A Spain kuwa, Barcelona na ci gaba da cin zaranta a saman teburi da maki 19 a mako na bakwai bayan da ta samu nasara a kan Real Sociedad da ci 2-1.  Ita kuwa abokiyar gabanta Real Madrid ta barar da wasanta inda ta sha kashi tamkar kurara roko a hannun Athletico Madrid, lamarin da ya sanya ta a matsayi na biyu da maki 18, yayin da Villareal ta lallasa Athletoco Bilbao da ci 1-0 tare da darewa a matsayi na uku da maki 16.

A Premier League, Liverpool da ke saman teburi ta baras da wasan da ta yi da Crystal Palace da ci 1-2 ba tare da yin tasiri a matsayinta na farko ba. Sai dai nasarar ta ba wa Crystal palace damar kasancewa a matsayi na uku da maki 11, bayan da Tottenham ta yi kunnen doki a wasanta. Ita kuwa Arsenal ta bi Newcasttle har gida kuma da doke ta da ci 2-1, lamarin da ya sa ta darewa a matsayi na biyu da maki 13 a mako na shida na lig din Ingila.

Wasan Pirimiya na IngilaHoto: Jon Super/AP Photo/picture alliance

A Faransa kuwa, PSG da dan wasanta ya lashe Ballon d' Or ta samu nasara a kan Auxerre da ci 2-0, yayin da Lyon ta doke Lille da ci daya mai ban haushi, lamarin da ke sa su yin kankankan a yawan maki, 15 kowacen su a mako na shida na babbn lig kwallon kafar Faransa.

Wasanni da aka yi a Afirka

A Jamhuriyar Nijar, duk da cewar kokawa na ci gaba da kasancewa wasa da ya fi samun karbuwa a kasar, amma gasar kwallon kafa na lokacin dogon hutun mkarantun boko da ake wa lkabi da TGV na jan hankalin matasa masu bugawa da masu kashe kwakwarkatn idanunsu.

Kungiyoyi daga unguwanni daban-daban da makarantu sun shafe makonni wajen buga gasar a tsakaninsu, kuma kowane gari, kowace jiha na shirya tata gasar, inda matasa ke nuna bajinta. A Gaya ga misali, a  jiya ne aka kawo karshen gasar kwallon kafa ta TGV, inda AS Transiteur ta yi nasarar lashe kofin a gaban AS Lycee.

Tseren keke a birnin Kigali na kasar RuwandaHoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

 An aka kammala gasar tseren keke ta duniya karo na 92 ​​a birnin Kigali na kasar Ruwanda, kuma Tadej Pogacar, dan kasar Sloveniya ya ci gaba da rike kambun da ya lashe a bara a kasar Switzerland. Tun sauran kilomita 100 da kammala wasa ne Pogacar ya tsere wa abokin hamayyarsa Remco Evenepoel dan Beljiyam da ya zo a matsayi na biyu.

Sai dai dan tseren keken na kasar Sloveniya Tadej Pogacar ya bayyana cewar ya ci karo da kalubale na hawa da gangara kafin hakarsa ta cimma ruwa.

'Yan tsere sama da dubu daga kasashe 110 ne suka halarci gasar tseren keke ta duniya da ya gudana a babban birnin kasar Ruwanda daga ranar 21 zuwa 28 ga watan Satumban 2025.

Zari ruga

Wasannin zari rugaHoto: Phil Walter/Getty Images for Rugby Australia

Ingila ta lashe kofin duniya na zari ruga na mata  bayan da ta doke Canada da ci 33-13 a ranar Asabar a birnin London. Wannan dai shi ne karo na uku da matan na Ingila suka samu kambun gasar cin kofin duniya na Rugby, baya da 1994 da 2014, tare da gudanar da wasanni 33 ba tare da doke su ba.

Sannan ba a taba samun cikar kwari na mutane 81,885 da suka taru don kwashe kwarkwatan idanunsu a wasan karshe na zari ruga na mata kamar wannan ba. Wannan ya kara wa Ingila kwarin gwiwa wajen kawar da bakin cikin rashin nasara da ta sha a baya, a gasar cin kofin duniya da ta gabata a 2022 a New Zealand.