1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU da Kanada za su hadewa Amurka kai?

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 17, 2026

Firaminista Mark Carney na Kanada ya nuna shirin amincewa da kasar ta shiga cikin kungiyar Tarayyar Turai EU, a matsayin mambae da ke da hadaka.

Tarayyar Turai | EU | Ursula von der Leyen | Kanada | Mark Carney
Firaministan Kanada Mark Carney da shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der LeyenHoto: Yves Herman/REUTERS

Wannan na zuwa a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya nuna fusata da yadda Kanada mai makwabtaka take kara raba gari da kasrasa a fannonin kasuwanci da rayuwa. Tun lokacin da Trump ya sake dawowa kan madafun iko, ya nuna yiwuwar amfani da karfi wajen hade kasar ta Kanada da Amurka.

Wannan ya haifar da turjiya daga bangarorin kasashen biyu, wadanda ke makwabtaka da juna. Firaminista Carney na Kanada ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Dokokin Tarayyar Turai, bayan ya gana da shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen da sauran jiga-jigan kungiyar tare da tabbatar da aniyar kasarsa wajen karfafa hulda da EU.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW