1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kare kanta game da rikitowar jirgin Ukraine

Zulaiha Abubakar
January 8, 2020

Firaministan kasar Justin Trudeau ya bukaci sanin abinda ya haifar da rikitowar jirgin saman Ukraine, bayan samun gawarwaki 63 na 'yan asalin kasar ta Kanada kamar yadda ministan sufurin kasar sanar.

Kanada_ Justin Trudeau in Brampton
Hoto: picture-alliance/A. Shivaani

Sanarwar ta kara da bayyana yadda samun cikakkun bayanai daga kasar Iran zai yi wahala sakamakon rufe ofishin jakadanci da Kanada ta yi a kasar ta Iran da kuma dakatar da harkokin jakadanci tun shekara ta 2012. Jirgin saman kasar ta Ukraine dai ya rikito ne mintuna kalilan bayan Iran ta harba makamai masu linzami a sansanin sojin Amirka dake Iraki da nufin daukar fansar mutuwar Janar Kassim Soliemani, kodayake mahukunta kasar ta Iran sun bayyana tangardar na'ura daga jirgin na Ukraine a matsayin abinda ya haifar da fadowar jirgin mai dauke da daliban kasashen ketare da kuma wasu iyalai.

Lokacin da yake hakurkurtar da iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa dasu ministan sufurin kasar ta Kanada Marc Garneau ya jaddada aniyar gwamnati ta shiga a dama da ita cikin binciken da kasar Iran zata fuskanta.