1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daukar mataki kan barayin waya a Kano

Nasir Salisu Zango LMJ
May 23, 2023

Al'ummar jihar Kano da wasu jihohin arewacin Najeriya da ake fama da masu amfani da makamai suna kwacewa mutane wayoyin hannu na salula, sun fara yunkurin daukar doka a hannunsu kan wadanda aka zarga da satar wayar.

Najeriya | Kano | Kwacen Waya
Kwacen waya ya addabi al'ummar jihar Kano da ke NajeriyaHoto: Muhammad Bello Ibrahim/DW

A jihar Kano dai tuni mutane suka fara yada shawarwarin cewar a rinka kashe barayin waya da zarar an kama su, kafin a mika su hannun hukuma. Tuni mutane da dama suka rasa ransu wasu kuma suka samu raunuka, sakamakon farmakin masu yin fashin wayar. Babban abin da ke ciwa mutane tuwo a kwarya shi ne yadda a lokuta da da ma idan an kama masu satar wayar sai a sake su, lamarin da yasa wasu mutanen suka fara yanke shawarar daukar doka a hannunsu wajen afkawa duk wanda aka samu da laifin yunkurin kwacen wayar. Abdulwahab Sa'id Ahmad matashi ne da ya taba fadawa hannun 'yan fashin wayar, ya ce tura ce ta kai bango shi yasa mutane suka fara daukar mataki.

Wasu kan dauki matakin boye wayoyinsu na hannu, domin gujewa barayiHoto: Muhammad Bello Ibrahim/DW

Barrista Abba Hikima Fagge lauya ne mai faftukar kare hakkin dan Adam a Kano, ya ce  rashin gamsuwa da matakan da mahukunta ke dauka ne ya sa aka fara  daukar doka a hannu. Sai dai ya ce, matakin zai iya haifar da gagarumar barazana. A nata bangaren rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce daukar doka a hannu haramun ne, a dangane da haka yake neman hadin kan jama'a domin kawo karshen wannan matsala. Kwanakin baya dai an yi musayar yawu tsakanin rundunar 'yan sanda da Hukumar Lura da Kotunan Kano, inda suke zargin juna da kawo tazgaro wajen dakile yunkurin 'yan fashin wayar. Sai dai fa tuni mutane sun fara afkawa duk wanda aka samu da wannan laifi, lamarin da ake ganin zai iya zama wata babbar barazana ga tsaro da zaman lafiya a jihar baki daya.