Majalisar malamai ta jihar Kano da ta kunshi manyan malamai da suka fito daga dariku dabam-dabam, sun yi kira da a rage gina Masallatai barkatai a fadin jihar.
Talla
Malaman na jihar Kano da ke Najeriya dai sun yi wannan kiran ne, a wani mataki na takaita matsalar rarrabuwar kai da ke neman kawo barazana ga addinin Musulumci da Musulmi a jihar. Matakin dai ya jawo korafe-korafe daga masana da sauran jama'a, inda wasu ke ganin hakan a matsayin wani yunkuri na dakile kaifin addini a jihar da ake ganin ta yi shura a fannin addinin Musulunci a duniya. Kiran na malaman ya zo ne bayan taron wuni biyu da Majalisar Malaman Jihar Kanon ta yi, tare da hadin gwiwar jami'ar Bayero da ke Kanon. Manyan malamai da ke wakilcin kungiyoyin addini a jihar da dama ne suka halarci taron, wanda aka fitar da matsaya a fannoni dabam-dabam.
Masallatai tara da suka shahara a Afirka
A birnin Dakar na kasar Senegal an yi bikin bude masallaci mafi girma a yammacin Afirka. Nahirya na alfahari da wuraren ibada masu yawa. Daga shekarar 670 zuwa 2019, masallatan sun dauki hankalin masu zanen gine-gine.
Hoto: Getty Images/R. Kramdi
Masallacin Massalikul Jinaan a Senegal
Sabon masallacin Massalikul Jinaan da aka kammala aikin gininshi a watan Satumban 2019, Majalisar Muridan Senegal ta yi aikin a kan kudi Euro miliyan 30. Shi ne mafi girma a Afirka ta Yamma, yana iya daukar masu ibada dubu 15 a ciki da wasu dubu 15 a harabarsa. Sunansa ya samo asalai daga taken wani adabi na Sheikh Ahmadou Bamba Mbacke, da ya kafa Majalisar Muridan a karni na 19.
Hoto: AFP/SEYLLOU
Babban masallacin Kairouan a Tunisiya
Wannan kasaitaccen masallacin na daya daga cikin mafi tsufa wuraren ibada a duniyar Musulmi, watakila ma mafi dadewa a Afirka. Janar na Larabawa Uqba ibn Nafi ya gina a shekarar 670. Ginin na nuna wata hadaka ta tasiri na tsarin gine-ginen farko na Muslunci da Romawa da kuma Byzantine. Masallaci yana a wurin tarihin duniya na UNESCO da ke a Kairouan, yankin Hamada na arewacin Tunisiya.
Hoto: Imago/Panthermedia
Masallacin Larabanga a Ghana
Masallacin da ake wa lakabi da Makkar Yammacin Afirka, masallacin Larabanga an gina shi ne bisa tsarin zanen gini na Sudan a Larabanga, Ghana. An gina shi a 1421– sh ne mafi dadewa a kasar kuma daya daga cikin masallatai mafi tsufa a Yammacin Afirka. Yana cikin jerin wurare 100 da ke fuskantar barazana,an yi masa gyare-gyare a lokuta da dama, abin da ya farfado da ilimkin ginin laka.
Hoto: Imago/UIG
Masallacin Touba a Senegal
Babban Masallacin Touba dan Sufi kuma Waliyi na Majalisar Muridai, Amadou Bamba ya aza tubalinsa a 1887, ko da yake a hukumance ba a gama gininshi ba sai a 1963. Bamba ya rasu a 1927, kuma yanzu zuri'arsa ce ke tafiyar da masallacin. Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin masallatai mafi kyau a duniya.
Hoto: Imago Images
Babban Masallacin Djenne a Mali
TBabban Masallacin Djenne shi ne mafi girma a duniya da aka gina da laka. An gina shi a 1907, an yi amfani da tsarin gine-gine da asali da yankin Sahel na yammacin Afirka a karni na 14. A kowacce shekara dukkan al'ummar garin Djenne na shiga cikin wani bikin gyara bangarorin da suka lalace sakamakon zaizayewar kasa. Ana kammala bikin da kide da abinci.
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani
Babban Masallaci kasa a Abuja, Najeriya
A 1984 aka gina wannan masallaci mai ban sha'awa da kuma ke zama babban masallacin kasa a Najeriya. Ko da yake an gina shi ne don Musulmi masu ibada, amma ana bude kofofinsa ga wadanda ba Musulmi ba a lokutan da ba a salla a ciki. Yana daura da ginin cibiyar Kiristoci ta kasa.
Hoto: Imago Images/F. Stark
Masallacin Ka a Yuganda
A 2006 da aka kammala aikin ginin Masallacin kasa a Yuganda da ke zama kyakkyawan misali na zanen ginin masallaci na zamani. Tsohon shugaban kasar Libiya Muammar Gaddafi ya kaddamar da shi sannan daga bisani aka sa masa sunansa. Bayan mutuwarsa an sake masa suna, shi ne kuma shalkwatar Majalisar Koli ta Musulmin Yuganda.
Hoto: Imago/UIG
Masallacin Hassan II a Maroko
An kammala ginin a 1993. Yanzu haka Masallacin Hassan II shi ne mafi girma anhiyar Afirka, kuma na uku a duniya baki daya. An gina masallacin ne don tunawa da cikar shekaru 60 na ranar haihuwar tsohon Sarki Hassan II. An gina shi a wani wuri da ke kallon teku da ke kuma nuni da wata ayar Al-Qurani da ke cewa an gina Al-arshin Ubangiji a kan ruwa.
Hoto: picture alliance/Arco Images
Masallacin Djamaa el Djazair a birnin Aljiyas
Masallacin da aka kuma sanshi da Babban Masallacin Aljiyas, an kare gininshi a bana bayan shekaru bakwai na aikin ginin da ya ci kudi kimanin Euro miliyan 915. Ginin na hadin gwiwa ne da tallafin kudi daga gwamnatin Aljeriya, da masu zanen gini na Jamus, kamfanin gine-gine na kasar China ya yi aikin. Hasumiyarsa ta kai mita 265, ita ce mafi tsawo a Afirka.
Hoto: Getty Images/R. Kramdi
Hotuna 91 | 9
Farfesa Babangida shi ne sakataren majalisar kuma shi ne ya isar da sakon, inda a ciki yake bayyana takaicin majalisar kan yadda wasu cikinsu suka dade da zama 'yan amshin shata wajen zubar da girmansu a gaban 'yan siyasa suna zubewa da yi musu bambadanci dan samun abin duniya. Kunshin matsayar malaman dai ta jawo kace-nace musamman ma batun shawarar rage Masallatai. inda har ma masu fashin baki kamar Abubakar Ibrahim ke ganin cewar wannan dai zance ne kawai da bai dace a jiyo shi daga malaman Kano ba. To amma ga Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale limamin Masallacin Jumma'a na Ihya'ussunah da ke gwammaja, ya ce wannan mataki shi ne daidai domin dama Musulumci ya yi hani da yawan bude Masallatan Jumma'a barkatai sai dai in akwai wani dalili kwakkwara.
Maganar Liman Babangwale ta yi daidai da ra'ayin Farfesa Sani Lawal Malumfashi masanin zamantakewar dan Adam a jami'ar Bayero da ke Kanon, wanda ya ce da ma can malamai ne ke kirkirar Masallatai domin tara magoya baya da sunan neman abin duniya, dan haka matakin kayyadewar yana kan turba. Amma fa a iya cewar an ki a yaba an koma na yaba, domin malaman ne da kansu suka fara karya dokar kiyaye gina Masallatai musamman na Jumma'a. A baya dai sai da izinin masarauta ake gina Masallacin, kafin daga bisani aka sami wasu daga Malamai suka yi wa waccan kai'dar bore.