1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Abba ne kenan ya samu nasara a shari'ar da aka yi?

November 22, 2023

A wani abun da ke zaman rudani a cikin shari'ar zaben Jihar kano, bangaren jam'iyyar NNPP ya ce kotun daukaka karar da ta Yi hukunci a Abuja su ta bai wa nasara bisa shari‘ar makon da ya shude:

Hoto: REUTERS

Ba dai kasafai a kan samu harshe irin na damo a cikin gidan alkalan Najeria ba.To sai dai kuma wata kotun daukaka karar zaben Jihar kano da ta zauna a Abuja na shirin barin baya da kura cikin hukuncin da ta yanke. Duk da cewar a cikin fatar baki, ra'ayi ya zo iri guda tsakanin alkalan, bisa halascin zaben Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC, can a rubuce kan takarda dai kotun ta tabbatar da zaben Abba Kabir na jam'iyyar NNPP da ke bisa mulki cikin jihar a halin yanzu. Abun kuma da ya jawo ka ce--na-ce dama musayar yawu a tsakanin bangarorin da ke gwagwarmayar neman ikon Jihar Kano. Barrister Haruna Isa Dederi dai na zaman kwamishinan shari'ar Jihar Kanon. Lauyan da ke cikin nadi a tsarin shari'a, ko kuma kokarin cika burin son rai, banbancin da ke tsakani na kalaman alkalan, dama rubutun da ke ta yawo a gari, bai isa sauya hukuncin shari'ar zaben ba, a fadar barrister Abdul fage da ke zaman mashawarcin shari'ar jam'iyyar  APC da ke Kano.

Wani sabon rikicin siyasa a Najeriyar bayan hukuncin kotun

Hukuncin da ke da harshe na damo, ko kuma kokari na boye gaske, sabon kiki kakar dake kasa dai a tunanin barrister Mohammed Shu'aib da ke zaman wani lauyan da ke a Abuja, tana iya kai wa ga warwara a zauren  kotun. Kuskure cikin gidan alkalai ko kuma son rai da kila ma cin hanci, sannu a hankali dai bangaren shari'ar Najeriyar na fuskantar kallon tsaf cikin jeri na hukuncin zaben da ke gudana yanzu. Bayan rushe zabukan Jihohi na Kano da Zamfara da Plateau dai, akwai zargin kokari na murde adawa da kila dora Najeriyar bisa turbar  jam'iyya guda daya.