1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soke yi mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara

Abdourahamane Hassane
March 5, 2021

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta amince da umarnin dakatar da mukabalar da aka shirya yi a ranar Lahadi da ke tafe  

Nigeria Ramadan
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Tun farko an shirya yin mukabalar ne tsakanin sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma malaman Kano da ke kalubalantar salon wa'azin malamin har ma wasu ke cewar yana keta alfarmar ma'aiki. Wata kotu a Kanon a karkashin mai shari'a Muhammd Jibril ta yanke hukuncin dakatar da wannan mukabala da ake shirin yi. Barrister Musa Abdullahi Lawal atoni janar kuma kwmaishinan shari'a na Jihar Kano ya tabbatar da hukuncin.