1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Kano ta dakatar da Abduljabbar

Nasir Salisu Zango LMJ
February 4, 2021

Kwana guda bayan umarnin rufe Masallacinsa da wurin karatunsa malamin nan Sheikh Dakta Abduljabbar Nasiru Kabara na Kano, ya yi martani dangane da matakin rufe Masallacin da wurin karantarwarsa.

Nigeria | Abduljabbar Nasiru Kabara | Kleriker
Sheikh Dakta Abduljabbar Nasiru KabaraHoto: Aliyu Samba

Baya ga rufe Masallaci da makarantun Sheikh Dakta Abduljabbar Nasiru Kabara da gwamnatin ta jihar Kano ta yi, ta kuma sanar da hana yada duk wani na'uin karatunsa ko da kuwa ta kafar internet ne. Wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafe da wasu malamai ke yi, na cewar wa'azin malamin ya sauka daga layi.

Malamin matasa?

Sheikh Abduljabbar Kabara dai malami ne da ya yi suna wajen yin wa'azi da tara matasa wajen gabatar da karatunsa. Sai dai kuma da yawan malaman jihar Kano na ganin cewar karatun nasa cike yake da keta alfarmar ma'aki da kuma cin fuska ga addinin musulunci, zargin da malamin kullum yake musantawa. Da yake martani kan wannan mataki da aka dauka na rufe masa Masallaci da hana shi wa'azi, Malam Abduljabbar ya ce ya rungumi kaddara. 
Dangane da batun zargin da ake masa na cin zarafi da keta alfarmar ma'aki kuwa, malamin ya ce a littattafan magabata ya gano kura-kurai kuma yake karanta su domin nuna cewar kalaman keta alfarmar ma'aki ne shi yasa yake fito da su yana karyata su. Wannan mataki dai ya jawo martani daga mutane da da dama ciki har da Abubakar Ibrahim wanda ke cewar wanan mataki tamkar an kashe maciji ne ba a sare masa kai ba.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

JIhadi ko take 'yanci?

To amma ga mutane kamar Aliyu Dahiru Aliyu mai fashin baki kan shari'ar Musulunci, ya ce wannan mataki ba ya kan ka'ida domin ya yi karen tsaye ga 'yancin fadin albarkacin baki. Sai dai kuma ga Sheikh Abdusalam Baban Gwale limamin Masallacin Jumma'a na Gwammaja a Kano, wanda kuma ya taba yin mukabala da Malam Abduljabbar kan tsarin karantawarsa, ya ce wannan mataki na gwamnati ya yi daidai domin jihadi ne. Duk da cewa dai Malam Abduljabbar ya ce ya karbi kaddara, amma jami'an tsaro na cikin shiri domin dakile duk wata tirjiya da ka iya biyo bayan wannan mataki.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani