1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kano na jimamin mutuwar 'yan majalisa 2 a rana daya

Nasir Salisu Zango ZUD/AH
December 24, 2025

Majalisar dokokin jihar Kano ta shiga alhini bayan rasuwar ’yan majalisa biyu a rana guda a harabar majalisar, ciki har da shugaban kwamitin kudi Aminu Sa’adu Ungoggo da Sarki Aliyu Daneji.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir YusufHoto: Nasiru Salisu Zango

Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Ungoggo kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar, Hon Aminu Sa'adu Ungoggo, ya rasu ne bayan da ya yanke jiki ya fadi jim kadan bayan isa harabar majalisar. An garzaya da shi asibiti, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Awa guda bayan sanar da rasuwar Hon. Aminu Ungoggo, sai kuma aka samu labarin rasuwar wani dan majalisar dokokin jihar, Hon Sarki Aliyu Daneji, mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano  da Kewaye.

Kawo yanzu dai jihar Kano na cikin jimami da alhini, yayin da jama'a da dama ke bayyana mamaki da alhinin rasuwar yan majalisun biyu a rana guda.